Waiwaye: Kashe masallata a Katsina, da rage farashin wankin ƙoda a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

A ranar Litinin ne aka wayi gari da labarin harin 'yanfashin daji da ya kashe sama da mutum 30 a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya yayin da suke tsaka da sallah a wani masallaci.

Wasu mazauna yankin Gidan Mantau na ƙaramar hukumar Malumfashi sun shaida wa BBC Hausa cewa lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin, inda tuni aka yi jana'izar mutum 28.

"Muna tsaka da sallah suka buɗe mana wuta, mutum 28 muka yi wa jana'iza ciki har da mahaifina," in ji wani mutum da muka ɓoye sunansa cikin kuka da share hawaye.

"A gida suka ritsa shi [mahaifin], suka kulle shi a ɗaki, suka zuba fetur kuma suka kunna wuta."

Ragi a farashin wankin ƙoda

A makon ne kuma Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya amince da rage farashin wankin ƙoda daga naira 50,000 zuwa naira 12,000 a manyan asibitocin tarayya a fadin ƙasar.

Daniel Bwala, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan Bayanan da suka shafi tsare-tsaren gwamnati ne ya bayyana hakan a shafin sada zumuntansa na X, inda ya ce matakin zai sauƙaƙa wa dubban marasa lafiya masu fama da ciwon ƙoda.

An fara aiwatar da wannan mataki a manyan asibitoci kamar FMC Ebute-Metta da ke Lagos da FMC da ke Jabi a Abuja da UCH Ibadan da FMC Owerri da UMTH Maiduguri, yayin da za a ƙara wasu kafin ƙarshen shekara domin samun damar amfani da su a duk faɗin ƙasar.

Shugaba Tinubu a baya ya amince da haihuwa ta hanyar tiyata kyauta a asibitocin gwamnati domin inganta lafiyar mata da rage mace-macen da za a iya hana faruwarsu.

Takun-saƙa tsakanin manyan sarakunan Yarabawa biyu

A ranar Litinin ne Alaafin na Oyo Oba Akeem Owoade ya bai wai Ooni na Ife Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi wa'adin sa'o'i 48 domin soke muƙamin sarauta na masauratar Okanlomo da ake zargin ya bai wa wani attajiri a Ibadan mai suna Dotun Sanusi, duk a ƙasar Yarabawa

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan harkokin ƴada labarai na Alaafin, Bode Durojaiye ya fitar.

Sanarwar ta ce: "Yanayin yanzu da ake ciki shi ne ya wajabta wa Alafin na Oyo ya bai wa Ooni na Ife wannan umarnin domin ya soke muƙamin sarautar da aka bai wa Injiniya Dotun Sanusi cikin sa'o'i 48 ko kuma ya fuskanci hukunci."

Sanarwar ta jaddada cewa, Alaafin ne kawai ke da ikon bai wa kowane mutum muƙamin sarauta da ya shafi duk fadin ƙasar Yarbawa wadda kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da hakan

"Takardar muƙamin da aka gabatar wa Oba Ogunwusi lokacin da aka naɗa shi ya takaita ikon ƙarfinsa kawai ga ƙaramar hukumar Oranmiyan, wadda yanzu ta rabu zuwa ƙaramar hukuma uku da suka haɗa da Ife ta Tsakiya da Arewacin Ife da kuma Kudancin Ife." sanarwar ta ƙara da cewa.

Haɗarin kwale-kwale a Sokoto

Aƙalla mutum 40 ne suka ɓace bayan haɗarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Lahadi.

Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumomin jihar suka bazama domin ceto waɗanda suka ɓacen.

Waɗanda lamarin ya shafa yawanci ƴan kasuwa ne da suke hanyar tafiya zuwa babbar kasuwar Goronyo da ke ci duk ranar Lahadi a lokacin da kwale-kwalen ya kife ɗauke da matafiya kusan 50, amma hukumomi sun ce an samu nasarar ceto mutum 10 a nan take.

Amma daga baya an samu nasarar ceto mafi yawan mutanen da suke ɓace ɗin.

Rasuwar Sarkin Zuru Muhammadu Sami

Sarkin Zuru Manjo Janar Muhammadu Sami II mai ritaya ya rasu yana da shekara 81 da haihuwa.

Sakataren yaɗa labarai na gwamantin jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa sarkin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Landan ranar Asabar da dare.

Sarkin tsohon gwamnan mulkin soja ne na jihar Bauchi lokacin mulkin marigayi Janar Muhammadu Buhari a 1984 zuwa 1985.

Sanarwar ta ce Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya siffanta marigayin a matsayin "uban ƙasa mai cike da hikima kuma wanda ya sanya hidimar al'ummarsa a gaba".

Sarkin ya rasu ya bar mata huɗu da 'ya'ya bakwai.

Ƴan Najeriya miliyan 31 na fuskantar matsalar ƙarancin abinci - MDD

Haka kuma a makon ne ofishin hukumar kula da jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna damuwa kan ƙaruwar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro a Najeriya, inda ta yi kiyasin cewa ƴan ƙasar miliyan 31 na fama da matsalar ƙarancin abinci.

Hukumar ta ce akwai sama da yara miliyan goma ƴan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Bayanin haka ya fito ne a taron da gwamnatin tarayya da hukumar suka gudanar yayin bikin ranar Jin-Ƙai ta Duniya na 2025, wanda aka gudanar ranar Talata a Abuja, mai taken "ƙarfafa haɗin gwiwa a duniya da kuma tallafawa al'ummomi".

Hukumar ta ce ya kamata a ɗauki matakai cikin gaggawa domin rage barazanar ƙaruwar matsalar.

Jami'in hukumar ta jin-ƙai a Najeriya, Mohamed Fall, ya bayyana cewa bikin ranar ta bana ya zo ne a daidai lokacin da ake samun raguwar bayar da taimakon jin-ƙai ga mabuƙata a duniya.

"Buƙatar jin-ƙai na ƙaruwa a Najeriya, sakamakon matsalar ƙarancin abinci da rashin abinci mai gina jiki. Yanzu akwai ƴan Najeriya miliyan 31 da ke fama da matsalar ta ƙarancin abinci," in ji shi.

Ba ma goyon bayan kara albashi ga masu rike da mukaman siyasa — ADC

Sabuwar jam'iyyar hadakar 'yan adawa a Najeriya ta ADC ta bayyana damuwa a game da shirin kara albashin masu rike da mukaman siyasa a kasar.

Jam'iyyar ta bayyana shirin da cewa ''yin biris ne'', kuma cin fuska ne ga al'ummar kasar da ke fama da katutun matsalolin rayuwa da suka hada da hauhawar farashin kaya da tashin farashin mai da kwauron albashi mafi kankanta da dai sauran matsaloli.

Daya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar hadakar ta ADC, Faisal Kabiru, ya shaida wa BBC cewa, duba da halin da talakan Najeriya ke ciki wanda abinci ke gagararsa ballantana magance wasu matsaloli na rayuwa, ace za a karawa mutanen da suke rayuwa yadda suke so saboda suna da hali albashi.

Ya kamata kowane ɗan Najeriya ya koyi dabarar kare kai - Musa

Wani labari da ya hankali a makon shi ne yadda babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya shawaraci ƴan Najeriya da su laƙanci dabarun kare kai daga haɗurra a matsayin mataki na ko-ta-kwana.

C.G Musa ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels a yau Alhamis.

Matsalar tsaro na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu.

Duk da cewa hukumomi na cewa suna bakin ƙoƙarinsu, amma lamarin na ci gaba da laƙume ɗaruruwan rayuka a yankunan da ake fama da irin waɗannan tashin-tashina, kamar arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma arewa ta tsakiyar ƙasar.

Lokacin da aka tambayi Christopher Musa kan ko ya kamata al'umma su koyi dabarun faɗa, ya ce "Ya kamata mutane su ɗauki wannan tamkar koyon tuƙi ne ko iyo, wannan abu ne da ake buƙata a rayuwa, ko da ana fama da yaƙi ko a'a".

"Ina ganin ya kamata a wayar da kan kowane ɗan Najeriya kan tsaro a kowane mataki. Kare kai na da matuƙar muhimmanci," in ji Musa.

Sai dai daga bisani ya sake fayyace jawabin, inda ya ce shi ba yana nufin ƴan ƙasar su mallaki makami ba ne.