Akwai yiwuwar mace ta ɗauki ciki da kanta bayan haihuwa ta hanyar dashen kwai

Asalin hoton, Shema
Damar samun juna-biyu na karuwa ga macen da ta samu haihuwa bayan yi mata dashen kwai, wanda ake kira IVF.
Akan samu haka a kusan daya cikin mata biyar da aka yi wa IVF.
Masu bincike sun ce wannan batu ne da ya kamata ma’aurata su sani.
Sun ce labari ne da zai iya kawo sabon tunani game da yadda za a tsara iyali.
Sun yi nazarin bayanai daga mata sama da 5,000 kafin samun matsaya.
A cewar hukumar kula da lafiya ta Birtaniya (NHS), damar mace ta kara daukar ciki ta hanyar da aka saba, shekara daya bayan haihuwa ta hanyar dashen kwai.
Idan sun kwashe shekaru su na nema, shi ne ɗaya cikin hudu, ko kasa da haka.
Yawanci ana gano rashin haihuwa ne bayan ma'aurata sun kasa samun ciki bayan sun yi shekara daya suna gwadawa.
Amma tun da yawan haihuwa na mace yana raguwa da shekaru, matan da suka haura 35, kuma duk wadanda suka san suna iya samun matsalar haihuwa, ya kamata su ga likitansu da wuri, bisa ga shawarar.
Matsalolin haihuwa na iya zama na dindindin ko na ɗan wani lokaci kuma suna iya shafar namiji ko mace.
Akwai abubuwa da kan jawo rashin haihuwa da za a iya magancewa, amma kusan daya cikin hudu na ma'aurata ba za su iya tabbatar da wani dalili ba.
Magungunan rashin haihuwa, irin su in-vitro (IVF), wato dashen kwai ba kodayaushe ake samun su kyauta ba akan tsarin NHS.
Kudin yin aikin matakin farko na IVF na iya kaiwa fan 5,000 ko fiye da haka.

Asalin hoton, Shema
An gano cewa Shema Tariq daga Landan, na fama da "rashin isasun ajiyayyun kwai", ma'ana kwayayen da suka rage a cikinta ba su da yawa, kuma zai yi wahala ta iya ɗaukar ciki ba tare da IVF ba .
Sai da aka yi mata aikin IVF har matakai shida, sannan ta dauki cikin danta, wanda aka haifa a cikin 2018.
Babban abin mamaki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Likitana ya fara yi min maganar maganin hana haihuwa jim kadan bayan na haihu, - amma sai duk muka fashe da dariya muna tunanin cewa ba shi da amfani," in ji Shema.
“Ban taba tunanin cewa zan iya daukar ciki ba, duk da kasancewa ta likitar lafiyar jima’i'', in ji ta.
"Shekarata 43, kuma an shaida min cewa damar da nake da ita ta ɗaukar ciki ta yi kasa da kashi 1%.
“Bayan wata takwas, ba zato ba tsammani sai gashi na dauki cikin ’yarmu.
"Hakan ya kasance wani babban abin mamaki - amma lokacin da muka fara ganowa, na dan shiga damuwa saboda ban shirya ɗaukar wani ciki ba.
"Da na san cewa daya daga cikin mata biyar suna daukar ciki bayan sun haihu ta dashen kwai, da na yi amfani da maganin hana haihuwa har sai na kasance a shirye ta kowanne fanni."
Jagorar sabon binciken, wanda aka buga a mujallar 'Human Reproduction', Dokta Annette Thwaites, ta Jami'ar College London, ta ce: "Bincikenmu ya nuna cewa daukar ciki bayan haihuwa ta hanyar IVF ba abin da aka saba gani ba ne.
"Wannan ya bambanta da tunanin da mata da masana kiwon lafiya ke yi a baya da kuma wadanda aka saba bayyanawa a kafafen yada labarai, cewa lamari ne mai wuyar gaske."
Binciken da ta gudanar tare da mambobin tawagarta 11 sun gano akalla daya daga cikin mata biyar sukan yi ciki ne a cikin shekaru uku bayan sun haihu ta hanyar amfani da maganin haihuwa. Kuma wannan ya shafi nau'o'i daban-daban da sakamakon maganin haihuwa.
Dokta Marta Jansa Perez, mai kula da lafiyar mahaifa, daga kungiyar haihuwa ta Birtaniya, ta ce: "Wannan binciken ya nuna muhimmancin bai wa marasa lafiya cikakken bayani game da yiwuwar daukar ciki a kowane lokaci, musamman bayan haihuwa ta hanyar IVF.
“Abin farin ciki ne cewa irin wannan adadi mai yawa na marasa lafiya suna iya daukar ciki bayan IVF, amma ya kamata mutane su san cewa a lokutan da shekarun mace ke haifar da rashin daukar ciki ko kuma a sami rashin haihuwa mai tsanani daga bangaren namiji.
Dan haka yana da kyau a nemi magani kan haihuwa na biyu cikin gaggawa.











