'Matar da ta yi ɓarin ciki sau 22'

Imtiaz Fazil ta dauki ciki har sau 24, sai dai yara biyu ne kadai ke raye a cikinsu.
Ta fara samun juna biyu a shekarun 1999. A tsawon shekaru 23, ta yi bari sau 17, inda yara biyar daga ciki kuma suka mutu kafin a rada musu suna saboda irin kwayoyin halitta da aka haife su da shi.
Matar mai shekara 49 da ta fito daga Levenshulme da ke birnin Manchester, ta fadawa wani shirin BBC cewa barin da ta yi abu ne da ba za a iya misaltawa ba, amma ya zama tilas ta fadi abin da ya faru da ita, saboda hakan ya zama maganar da ake ta yi tsakanin kungiyoyi a Kudancin Asiya.
Ta ce tana son kawar da batun nan da mata ke da shi na jin kunyan fitowa su fadi ‘ya’yan da suka rasa.
Imtiaz ta kara da cewa ‘yan uwanta ba sa yi mata magana a kan ɓarin da ta yi saboda suna ganin hakan zai ɓata mata rai ta hanyar tunowa da shi.
''Abin ba shi da dadi sam, shiya sa babu wanda ke min magana a kan batun,’’ in ji Fazil.
Ta kuma ce duk da cewa ta samu bari da yawa, babu wanda ya taɓa tambayarta ya take ji ko kuma cewa ko tana tunanin yaran da ta rasa.
"Babu ranar da ba na tunanin ‘ya’yana da na rasa,’’ a cewar Fazil.

Asalin hoton, FAMILY HANDOUT
Sarina Kaur Dosanjh da mijinta Vik, suma suna fatan cire tsoro ta hanyar fitowa su yi magana kan mutanen da suka rasa ‘ya’yansu.
Sarina mai shekara 29, da ta fito daga Walsall da ke yammacin Midlands, ta kirkiro da wata kungiyar agaji mai suna Himmat Collective, da zai bai wa matan Kudancin Asiya da kuma mata damar su fito su fadi ‘ya’yan da suka rasa.
Ma’auratan, wadanda suka samu bari sau biyu a cikin shekaru biyu, sun ce radadi baya barin wasu su yi magana a kan batun. ‘‘Ina ganin mutane na boye batun,’’ a cewar Sarina.
Ta ce akwai kuma batun da ake cewa duk matar da ke da ciki, ya kaurace wa duk wacce ta taba bari saboda hakan zai iya shafarta.
"Wannan wani tsangwama ne da ya kamata a kawo karshenta,’’ a cewar Sarina.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Vik ya ce ya samu martani daban-daban game da magana kan ɓarin ciki.
Ya ce duk da cewa wasu maza sun faɗa masa cewa ya taimaka musu wajen mantawa da rashin, wasu kuma ce masa suka yi wannan ba abu ba ne da ya kamata a rika magana a kansa.
Sai dai, ya ce yana da yaƙinin cewa muddin aka riƙa magana kan batun, to za a iya samun mafita.
''Ya kamata al’ummarmu su gane cewa ba abin kunya ba ne idan suka yi bari ko kuma suka rasa ‘ya’yansu,’’ in ji Sarina.
Imtiaz da Sarina sun ce suna fatan ganin cewa mutane za su dauki hakan a matsayin abu da aka saba ta hanyar yin magana a kai ba tare da jin kunya ba.
Imtiaz ta ce har yanzu tana cikin raɗaɗin rasa ‘ya’ya 22, sai dai ta ce tana son taimaka wa wasu da ke cikin irin wannan yanayi da shawarwari.
"Kada ku saka abin a cikin zuciyarku," in ji Imtiaz.
"Idan kuka yawaita tunani kan batun, zai haifar muku da damuwa.
"Ya kamata ku fito ku yi magana kan irin yanayi da kuke ciki, in ba haka ba ku samu matsala."












