Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bayern Munich ta fasa sayar wa Man U da de Ligt da Mazraoui,West Ham na zawarcin Rodriguez
Bayern Munich ta yi watsi da tayin hadin gwiwa da Manchester United ta yi mata domin sayan dan wasan tsakiyar Netherlands Matthijs de Ligt, mai shekara 24 da dan wasan bayan Moroko, Noussair Mazraoui mai shekara 26. (Telegraph - subscription required), external
Newcastle na shirin fara tattaunawa kan sabon kwantiragi da dan wasan gefen Ingila Anthony Gordon dan shekara 23 bayan ya dawo daga hutun gasar cin kofin Euro na bana da aka kamala a baya baya nan. (Athletic - subscription required), external
West Ham na kokarin daukar dan wasan tsakiya na Argentina Guido Rodriguez, mai shekara 30, bayan ya bar Real Betis. (Standard), external
Fulham na zawarcin dan wasa baya na Aston Villa da kuma Brazil Diego Carlos mai shekara 31. (Mail), external
QPR da Celtic na sha’awar dan wasan baya na Liverpool da Welsh Owen Beck dan shekara 21. (Sky Sports), external
Ita ma Arsenal na zawarcin dan wasan gaba na Brighton da kuma Brazil Joao Pedro dan shekara 22. (Football Transfers), external
Dan wasan baya na Villarreal da kuma Sfaniya Jorge Cuenca, dan shekara 24, na gab da komawa Fulham. (Sky Sports), external
Dan wasan tsakiyar Rennes Desire Doue,dan shekara 19, na son ya koma Bayern Munich a maimakon tsayawa a mahaifiyarsa ta Faransa tare da Paris St-Germain. (Sky Germany), external
Inter Milan ta bi sahun West Ham wajan daukar dan wasan baya ta gefen dama na Ingila Aaron Wan-Bissaka dan shekara 26 daga Manchester United. (Football Insider), external
Bournemouth na nazari kan dan wasan gaba na Aston Villa da Ingila Cameron Archer dan shekara 22,a matsayin wanda zai maye gurbin Dominic Solanke mai shekara 26, idan aka sayar da shi ga Tottenham (Football.London), external
Tottenham ta fasa sayan Federico Chiesa, dan shekara 26, daga Juventus duk da cewa rahotani sun alakanta kungiyar da dan wasan gaban Italiya . (Football Insider), external
Aston Villa ta gabatar da wata bukata a gaban Sunderland domin sayan dan wasan gaban kungiyar da kuma Ingila, Mason Cotcher dan shekara 17. (Fabrizio Romano), external
Manchester City ta amince ta bada aron dan wasan baya Finland Tomas Galvez dan shekara 19 ga zakarun Austria LASK. (Teamtalk), external