Fulham ta kammala ɗaukar Smith Rowe daga Arsenal

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Fulham ta sanar da sayen ɗan wasan tsakiya na Arsenal Emile Smith Rowe kan farashin da ake tunanin zai kai fam miliyan 27, a tashin farko.

Duk da yake Cottagers ba su bayyana jimillar kuɗin ɗan wasan mai shekaru 24 ba, an fahimci yarjejeniyar za ta iya kai wa £34m.

Smith Rowe wanda ya koma Arsenal tun yana ɗan shekara 10, ya fara wasa a babbar tawagar ƙungiyar a lokacin da ya ke da shakara 18 kuma ya zuwa yanzu ya buga wasanni 80 a gasar firimiya inda ya zura ƙwallaye 12.

Ya buga wa Ingila wasanni uku, kodayake wasansa na ƙarshe a tawagar ya zo ne a watan Maris 2022.

"Yanzu dai na iso nan, don haka ina matuƙar farin ciki da ni da iyalina" in ji Smith Rowe.

Fulham ta kuma ƙulla yarjejeniya da Ryan Sessegnon na tsawon shekaru biyu bayan kwantiraginsa ya kare a Tottenham.

Har ila yau ƙungiyar na ƙoƙarin ɗaukar ɗan wasan tsakiyan Manchester United Scott McTominay, bayan ta miƙa wa United tayi na biyu, wanda ake tunanin ya kai fam miliyan 20, kan ɗan wasan na Scotland mai shekaru 27.