Barcelona ta kai da kyar a gidan Rayo a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Rayo Vallecano da Barcelona sun tashi 1-1 a wasan mako na 14 a La Liga da suka kara ranar Asabar.
Rayo ce ta fara cin kwallo ta hannun Unai Lopez tun kan hutu, inda Barca ta mamaye karawar musamman zagaye na biyu da barar da damarmaki.
Daga baya ne Rayo ta ci gida ta hannun Florian Lejeune, wanda ya ji matsi daga wajen Robert Lewandowski.
Barcelona, wadda kawo yanzu take ta ukun teburi na fatan Real Madrid wadda za ta fuskanci Cadiz ranar Lahadi, kada ta ci wasan domin kada ta yi mata nisa.
Girona wadda ke jan ragamar teburin La Liga a kakar nan da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao ranar Litinin.
Barcelona ta yi amfani da sabbin 'yan wasa shida daga wadanda ta ci Alaves daga nan aka je buga wasan kasa da kasa.
Mai tsaron ragarta, Marc-Andre ter Stegen bai yi wasan ba, sakamakon jinya da yake yi.
Inaki Pena ne ya maye gurbinsa a karawar da suka raba maki.
A makon da za mu shiga Barcelona za ta karbi bakuncin Porto a Champions League, sannan ta kece raini da Atletico Madrid a makon farko cikin Disamba a La Liga.











