Manomin strawberry da isar tawagar Ghana zuwa Abidjan don gasar Afcon cikin hotunan Afrika

Wani dan wasan sukuwa tare da doki  a wani wasan sukuwa da aka yi a bakin teku a garin Cape Town na kasar Afrika ta kudu

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Masu hawan doki sun je bakin teku a garin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a ranar Juma'a
An wallafa
Wani manomi dan kasar Masar yana rike da strawberries da aka girbe a kauyen Al Deir da ke Toukh a birnin Alkahira.

Asalin hoton, KHALED ELFIQI/EPA

Bayanan hoto, Wani manomin strawberry ya baje-kolin amfanin gonarsa a arewacin Masar ranar Litinin.
 Kiristocin Orthodox sun hallara a dandalin Meskel domin bikin Kirsimeti a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Asalin hoton, DANIEL TEREFE/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Kiristoci mabiya darikar cocin gargajiya ta Orthodox a Habasha sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti a ranar Talata a dandalin Meskel na Addis Ababa.
Abune Fnauel, Archbishop na cocin gargajiya ta ‘yan Habasha da ke Washington DC na Cocin, shine ya jagoranci bikin Kirsimeti a cocin  Debre Meheret Kedus Michael Katolika Cathedral na Habasha.

Asalin hoton, ROB HILL/THE WASHINGTON POST/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A wannan rana, su ma mabiya cocin Orthodox da ke zama a ƙasashen waje sun yi taron adu'o'i a cocin da ke Washington DC babban birnin Amurka.
Mohamed Aqueel Ambraram  ya canza tufafinsa  gabanin wasan da ‘yan  Circus Galassia a Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu

Asalin hoton, KIM LUDBROOK/EPA

Bayanan hoto, Wani ɗan wasan Circus Galassia, Mohamed Aqueel Ambraram ya sauya tufafinsa gabanin wasan da zai yi a Johannesburg
Yar  wasan kwaikwaiyo  da kawa yar kasar Senegal da Amurka Anna Diop ta halarci bikin kadddamar da  wani fim da ake kira The Book of Clarence

Asalin hoton, CAROLINE BREHMAN/EPA

Bayanan hoto, A ranar Litinin 'yar wasan kwaikwayo da ƙawa, 'yar kasar Senegal da Amurka, Anna Diop ta halarci bikin ƙaddamar da fim din 'The Book of Clarence' a Los Angeles
Mutane sun  kai ziyara kasuwar  Amazigh a ranar 10 ga watan Janairu ya yin da Algeria ta gudanar da shagulgulan sabuwar shekarar Yennayer 2974

Asalin hoton, BILLEL BENSALEM/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Al'ummar Amazigh na gudanar da bikin sabuwar shekara, inda suke sayar da abinci da sauran kayayaki a wata kasuwa a ranar Laraba
Wata 'yar Somaliya  ta rike tutar Somaliya  a wani gangami

Asalin hoton, FEISAL OMAR/REUTERS

Bayanan hoto, 'Yan Somaliya sun yi zanga- zanga a Mogadishu domin nuna rashin amincewa da yarjejeniyar da ta ba Habasha damar amfani da wani yanki na tekun Somaliland na tsawon shekara 50
 Wani mai sayar da takalma  da rigunan ‘yan wasa kwallon kafar Ivory Coast

Asalin hoton, SIA KAMBOU/AFP

Bayanan hoto, Masu sayar da kayayyaki a Abidjan sun fara ciniki gabanin gasar kwallon kafar nahiyar Afrika da ƙasar ke karɓar baƙunci
 Tawagar kwallon kafa ta a filin jirgin sama Felix Houphouet-Boigny International a Abidjan.

Asalin hoton, ISSOUF SANOGO/AFP

Bayanan hoto, Tawagar ƙungiyar ƙwallon kafar Ghana ta isa Abidjan a ranar Laraba. Ghana za ta fafata da Cape Verde a wasanta na farko a ranar 14 ga watan Janairu
Hauren giwayen da aka kwace daga masu safarar namun daji

Asalin hoton, EMMANUEL OSODI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A ranar Talat Jami'an tsaron Najeriya suka lalata tarin hauren giwaye da aka kwato daga ƙasashen Afirka daban-daban da darajarsu ta kai kimanin dala miliyan 11.
Afrika ta Kudu

Asalin hoton, ESA ALEXANDER/REUTERS

Bayanan hoto, Lauyoyi da alummar ƙasar Afrika ta Kudu sun hallara a gaban wata kotu da ke Cape Town domin mara wa gwamnatin kasar baya, yayin da ta shigar da ƙara a gaban Kotun Duniya a birnin Hague inda take tuhumar Israi'la da aiwatar da kisan ƙare-dangi kan Falasɗinawa
Yana cikin wadanda suka yi gwagwarmayar kwato yancin bakar fata na kasar Afrika ta Kudu

Asalin hoton, SIPHIWE SIBEKO/REUTERS

Bayanan hoto, An kunna kyandir kusa da hoton babban mai ɗaukar hoto ɗan ƙasar Afirka ta Kudu Peter Magubane a wajen jana’izar sa ranar Laraba.