Hukumar Kwallon Ƙafar Ingila na tuhumar Van Diyk

Virgil van Dijk

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi kyaftin din Liverpool Virgil van Dijk da aikata abin da bai dace ba, bayan da aka ba shi jan kati a wasan da Liverpool ta doke Newcastle.

An bai wa kyaftin din Liverpool jan kati kai tsaye a minti na 29 da fara wasa a filin wasan St James’ Park a ranar Lahadin da ta gabata saboda keta da ya yi wa dan wasan Newcastle Alexander Isak.

Dan wasan ya yi ta jayayya da alkalin wasa John Brooks yayin da VAR ta sake duba lamarin.

Hukumar FA ta ce ana zargin Van Dijk da yin kalaman ɓatanci.

Dan wasan bayan Netherlands mai shekaru 32, wanda kuma ya yi jayayya da mataimakin alkalin wasa yayinda yake fita daga filin wasan, yana da har zuwa ranar Juma'a don amsa tuhumar.

A halin yanzu, an dakatar da Van Dijk na tsawon wasa daya saboda jan kati na farko sannan kuma ba zai buga wasan Liverpool na gaba da Aston Villa ranar Lahadi ba.