Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta zaftare rabin albashin Werner, Depay na kan hanyar komawa Juventus
Real Madrid na yin tuntuba kan yiwuwar sayo Armanso Broja, dan wasan gaba na Chelsea mai shekara 20 kuma dan kasar Albaniya, wanda tun kakar wasa ta bara ke buga wasanninsa a Southhanmpton a matsayin dan aro. (Standard)
Dan wasan baya na Bayern Munich Benjamin Pavard, mai shekara 26, na iya komawa Chelsea idan suka yi kwakkwaran tayi. (Bild)
Dan wasan gaba na Chelsea Timo Werner, mai shekara 26, ya amince a zaftare rabin albashinsa domin ya koma RB Leipzig a matsayin dan wasa na aro. (Bild - in German)
Dan wasan Barcelona kuma dan kasar Netherlands Memphis Depay, mai shekara 28, na cikin 'yan wasan da Juventus ke kallon za su taka wata muhimmiyar rawa nan gaba, inda ta ce Alvaro Morata mai shekara 29 ma yana cikin 'yan wasan da ta ke sha'awar mallaka. (Fabrizio Romano)
Juventus na son sayen Anthony Martial daga Manchester United, sai dai kocin Red Devils Erik ten Hag ya kafe na zai rabau da dan wasan gaban mai shekara 26 ba. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United ta gana da wakilin Benjamin Sesko, dan wasan gaba na Red Bull Salzburg mai shekara 19, inda take son raba dan kasar Sloveniyan da kungiyarsa. (Manchester Evening News)
Sai dai Salzburg na bukatar a ba ta akalla yuro miliyan 65 kafin ta mika Sesko, wanda ya zarce yawan kudin da United ke iya biya kan dan wasan gaban.. (Telegraph - subscription required)
Manchester City ta musanta cewa za ta sayar da Bernardo Silva dan wasan tsakiya mai shekara 27 ga Barcelona. (Mail)
Shugaban Kungiyar Barcelona Juan Laporta ya ce akwai yiwuwar Frenkie de Jing, dan wasan tsakiya mai shekara 25, wanda Manchester United ke son dauka zai yi zamansa a kungiyar, kuma ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin ya hana dan wasan dan kasar Netherlands tafiya. (CBS Sports)