Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Community Shield: Wa zai yi nasara tsakanin Man City da Liverpool?
Maki daya ne a kakar da ta wuce da Manchester City ta dauki Premier League tsakaninta da Liverpool wadda ta yi ta biyu.
Kungiyoyin biyu sun yi cefane a bana, don ganin sun taka rawar gani - wasu 'yan wasan City da na Liverpool sun koma wasu wuraren don gwada sa'a.
Ana kuma sa ran kungiyoyin za su taka rawar gani a kakar da za a fara cikin watan Agusta.
Ranar Asabar City da Liverpool za su fafata a Community Shield a filin wasa na Leicester wato King Power.
Kafin su kara BBC ta yi duba na tsakanin kan yadda kungiyoyin suka yi shirin fara tunkarar kakar bana ta 2022/23.
Sabbin 'yan wasan da suka dauka
Ba a yi kamfar cin kwallaye ba a gasar Premier League da ta wuce, inda City ta zura 99 a raga, Liverpool ta ci 94, Chelsea wadda ta yi ta uku 76 ta ci.
Kuma dukkansu sun kashe kudi mai yawa sun sayo 'yan wasan da za su taimaka musu wajen cin kwallaye a kakar nan.
City ta dauki Erling Haaland daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 51.
Dan kasar Norway mai shekara 22, ya nuna kwarewa a zazzaga kwallaye a raga a kungiyarsa da kasarsa.
Haaland ya zura kwallo 20 a wasa 21 da ya yi wa Norway ya kuma bar Dortmund bayan cin kwallo 86 a wasa 89.
Ana kuma sa ran dan kwallon Argentina, Julian Alvarez zai taka rawar da ta dace.
City ta mallaki dan wasan mai shekara 22 a watan Yunin bara daga River Plate, amma ta bar shi a can domin buga wasannin aro.
Yanzu da ya koma Etihad ana sa ran shi ne zai maye gurbin Sergio Aguero.
Haka kuma Pep Guardiola ya kara karfin masu buga masa tsakiya, inda ya dauko dan kwallon Ingila, Kalvin Phillips, mai shekara 26 daga Leeds kan fam miliyan 45.
Babban cefane da Liverpool ta yi a bana, shi ne sayen dan kwallon Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica a matakin mafi tsada a tarihinta kan fam miliyan 85.
Mai shekara 23 ya lakanci kwallon nahiyar Turai nan da nan, bayan da Benfica ta saye shi daga kudancin Amurka, wanda ya ci mata kwallo 34 a wasa 41 a gasar Portugal.
Haka kuma kungiyar Anfield ta dauki matashin tawagar Portugal, Fabio Carvalho daga Fulham da mai shekara 18 dan kwallon Scotland, Calvin Ramsay daga Aberdeen.
'Yan wasan da suka bar kungiyoyin a bana
Liverpool na bukatar kara karfi a gurbin masu ci mata kwallaye, bayan da Sadio Mane ya koma Bayern Munich, bayan cin kofi shida a Anfield.
Duk da cewar an yi wa dan kwallon tawagar Senegal, mai shekara 23 tayin kwantiragi mai tsoka don ya ci gaba da zama a Anfield, amma ya zabi komawa Jamus.
Ya koma Bayern Muich kan fam miliyan 35, hakika gasar Premier League ta yi rashin zakakurin dan kwallo.
Sauran da suka bar Liverpool a bana sun hada da Divock Origi da kuma Takumi Minamino.
Babban dan wasa da ya bar Manchester City a kakar nan shi ne Raheem Sterling.
Dan wasan tawagar Ingila ya koma Chelsea kan fam miliyan 50 a watan Yuli, ya bar Etihad bayan cin kwallo 131 a wasa 339 har da 13 da ya zura a raga a kakar Premier League da aka karkare.
Haka kuma City ta rasa wani dan kwallon, Gabriel Jesus wanda ya koma Arsenal a kakar nan kan fam miliyan 45.
Dan wasan Brazil bai wani yi kaurin suna ba a cin kwallaye a kungiyar ta Etihad - ya ci 58 a wasa 159 a Premier League - ya bayar da takwas aka zura a raga a bara a lik.
Bajintar da ya yi ya sa shi kan-kan-kan da takwaransa Kevin de Bruyne a babbar gasar tamaula ta Ingila da City ta lashe a kakar da aka kammala.
Wasannin sada zumunta don tunkarar kakar bana
Babu damar da za a auna kwazon kungiya a wasannin sada zumunta da ta buga, musamman an kusan fara gasar kofin duniya cikin watan Nuwamba 'yan wasa na dari-dari kada su ji rauni.
Sai dai kuma dama ce da kungiyoyin za su baje kolin 'yan wasan da suka dauka don sanin gurbin da ya kamat su buga, sannan magoya baya su auna kwazonsu.
Liverpool ta je buga wasannin sada zumunta a Asia da a cikin Turai, ita kuwa Manchester City Amurka ta yi nata wasannin.
Liverpool ta fara da shan kashi a hannun Manchester United da 4-0 a Thailand - wasan da Nunez ya fara yi wa kungiyar Anfield.
Daga nan Liverpool ta ci Crystal Palace 2-0 a Singapore, inda Jordan Henderson da Mohamed Salah suka ci mata kwallayen sai Nunez ya zura hudu a ragar RB Leipzig.
Sai dai Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Red Bull Salzburg, inda aka sauya Nunez a karawar ta ranar Laraba.
Ita kuwa City, ta yi wasa biyu na sada zumunta don tunkarar kakar bana a Amurka - daya da Club America da kuma Bayern Munich.
Ta fara da cin Club America 2-1, sannan ta yi nasara a kan Bayern Munich da ci 1-0, kuma Haaland ne ya ci mata kwallon a minti na 12 da fara wasan sada zumuntar.
Community Shield da kungiyoyin biyu za su kara ranar Asabar zai fayyace 'yan wasan da City da Liverpool za su yi amfani da su a kakar bana.
Da zarar sun gama wasan, mako daya tsakani za a fara gasar Premier League kakar 2022/23.
Shin ko wa zai lashe kofin bana?
Wadanne kungiyoyi ne za su samu gurbin gasar Zakarun Turai?
Wace kungiya ce za ta dauki FA Cup?
Wace kungiya ce za ta ci League Cup?