Madrid na zawarcin Garnacho, AC Milan na son Ziyech

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na kwaɗayin ɗan wasan Manchester United mai shekara 18 Alejandro Garnacho ɗan ƙasar Argentina wanda ya ci ƙwallonsa ta farko a gasar Premier a wasa da Fulham a watan da ya gabata. (Revelo - in Spanish)
Haka kuma United ɗin na ƙoƙarin ƙulla yarjejeniya da golan Borussia Monchengladbach da Switzerland Yann Sommer mai shekara 33 don a same shi a kyauta a kaka mai zuwa. (ESPN)
Real Madrid ta amince da wata yarjejeniya ta shekara shida da ta kai fam miliyan 62 domin sayen ɗan wasan Brazil Endrick daga Palmeiras sai dai ɗan wasan gaban mai shekara 16 ba zai je kulob din ba sai Yulin 2023 a lokacin da zai cika shekara 18 da haihuwa. (Fabrizio Romano)
A shirye AC Milan take ta yi ciniki da Chelsea kan ɗan wasan gaban na Chelsea Hakim Ziyech mai shekara 29 wanda ya taka rawar gani a Gasar Cin Kofin Duniya da ake yi a Qatar. (Gazzetta dello Sport via Football Italia)
AC Milan za ta bai wa ɗan wasan gaban Portugal Rafael Leao mai shekara 23 wa'adi zuwa Janairu domin ya sa hannu kan sabuwar yarjejeniya ko ya tafi. (Calciomercato - in Italian)
Shugaban Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi ya bayyana cewa ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford mai shekara 25 zai iya zama wanda suke hari a kaka mai zuwa. (Sky Sports)
Bayan cin ƙwallaye uku a gasar cin kofin duniya, ɗan wasan Ingila Rashford ya bayyana cewa babu abin da ya kai ya ci wa ƙasarsa ƙwallo. (Mirror)
Al-Khelaifi ya kuma ce yana da yaƙinin ɗan wasan gaban Argentina Lionel Messi mai shekara 35 zai ƙara tsawaita zamansa a Paris domin tattauna makomarsa a watan Janairu. (Sky Sports)
Arsenal za ta duba yiwuwar yin wasu abubuwa bayan ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus ya samu rauni a gwiwarsa a gasar kofin duniya, kamar yadda kocin kulob ɗin Mikel Arteta ya bayyana. (Football London)
Ɗan wasan tsakiyar Leicester da Ingila James Maddison mai shekara 26 shi ne na farko a jerin ƴan wasan da Newcastle ke hari a kaka mai zuwa. (90 min)










