Garnacho ne gwarzon ɗan kwallon Man United na Disamba

Alejandro Garnacho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Alejandro Garnacho ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon kafa na watan Disamba a Manchester United.

Mai shekara 19 ya lashe kyautar karo na biyu a jere, bayan da aka zaɓe shi fitaccen ɗan wasan Man United a watan Nuwamba.

A cikin watan na Disamba, ɗan wasan tawagar Argentina ya ci kwallo biyu ya bayar da biyu aka zura a raga, shi ne ɗan kwallon da ya taka rawar gani a wasan United da Aston Villa ranar 1 ga Kirsimeti.

A fafatawar Gernacho ya ci Villa kwallo biyu, sannan Rasmus Hojlund ya ci a 3-2 da suka tashi a gasar ta Premier League.

Alejandro ya samu kuri'a kashi 64 cikin ɗari a takarar da ya yi da Jonny Evans da kuma Kobbie Mainoo a kyautar ta watan Disamba.

Wannan shi ne karon farko a kakar nan da ɗan wasa ya lashe kyautar karo biyu a jere, bayan da ɗan kwallon tawagar Argentina ke ƙara nuna kansa a fannin tamaula a duniya.

A cikin watan Disamba ya bayar da kwallo biyu aka zura a raga ta farko a wasa da Chelsea, inda ya bai wa Scott McTominay ya zura a raga.

Ta biyun kuwa ita ce wadda ya bai wa Marcus Rashford ya ci Nottingham Forest a gasar Premier League da aka doke Man United 2-1.

Ranar Litin Manchester United za ta buga FA Cup karawar zagaye na uku.

Tuni aka fitar da Man United daga Carabao Cup na bana da kuma Champions League.