United na fatan sayen Hojlund kafin fara Premier League ta bana

Rasmus Hojlund

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United na fatan daukar dan kwallon Atalanta, Rasmus Hojlund kafin a fara Premier League ta kakar bana.

United za ta fara wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila da Wolverhampton ranar 14 ga watan Agusta.

Bayan da Real Madrid ta ci United 2-0 a wasan sada zumunta, Erik ten Hag ya ce suna ta kokarin sun dauki sabon dan wasa mai cin kwallo.

Hojlund shi ne kan gaba daga jerin wadanda United ke son dauka, amma kungiyar tana da wani zabin koda cinikin dan wasan mai shekara 20 bai yiwuba.

Haka kuma United na son sayen dan kwallon Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani da na Ajax, Mohammed Kudus.

Dan wasan tawagar Ghana zai iya buga gurbin masu taka leda daga tsakiya da kuma gurbin mai cin kwallaye.

Watakila United ta samu damar sayen Hojlund, bayan da Atalanta ke daf da kammala cinikin El Bilal Toure daga Almeria, don maye gurbin dan kasar Denmark.