Sorloth ya ci ƙwallo uku rigis a ƙanƙanin lokaci a tarihin La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Atletico Madrid, Alexander Sorloth ya ci ƙwallo huɗu a cikin minti 30, bayan doke Real Sociedad 4-0 a La Liga ranar Asabar.
Ɗan wasan tawagar Norway ya kammala zura uku rigis a raga a minti na 11, shi ne tarihin cin ƙwallo uku rigis a ƙanƙanin lokaci a La Liga, daga baya ya kara na huɗu.
Atletico Madrid, wadda ba ta cikin takarar lashe La Liga na bana, tana mataki na ukun teburi da maki 70, kuma saura wasa uku suka rage mata a kakar nan.
Barcelona ce ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki tara tsakani da Atletico, yayin da Real Madrid ta biyu ta bai wa abokiyar hamayya atletico tazarar maki biyar.
Ranar Lahadi za a buga El Clasicco tsakanin Barcelona da Real Madrid a wasan mako na 34 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ta doke Real Madrid a La Liga a cikin watan Oktoba a Santiago Bernabeu, sannan ta lashe Spanish Super Cup a watan Janairu a Saudiya.
Haka kuma Barcelona ta ɗauki Copa del Rey a kan Real Madrid a cikin watan Afirilu.
Real Sociedad tana ta 12 a teburin La Liga da maki 43.










