Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Conte na son Roma wadda za ta rabu da Mourinho, Man Utd na son Guehi
Ana sa ran Jose Mourinho ya bar Roma idan wa'adin aikinsa ya ƙare a ƙarshen kakar nan, kasancewar babu shirin tattaunawar tsawaita aikinsa na kociyan. (Sky Sports Italia daga Football Italia)
Shi kuwa tsohon kociyan Juventus, da Chelsea da Tottenham Antonio Conte wanda ya yi watsi da tayin zama kociyan ƙasar Saudiyya, ya ce yana son wata rana ya zama mai horad da Roma ko Napoli. (Il Corriere della Sera daga Football Italia)
Manchester United na son sayen matashin ɗan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 23 wanda kuma ake alakantawa da ƙungiyoyin Premier da dama. (Football Insider)
Mai yuwuwa attajirin nan mai harkar banki na ƙasar Qatar, Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani ya karkata wajen sayen Tottenham bayan da ya janye daga shirin sayen Manchester United. (Mirror)
Juventus na ci gaba da sa ido a kan ɗan wasan tsakiya na Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, wanda Tottenham ta yi wa farashin fam miliyan 30, wanda kuma Atletico Madrid ma na sonshi. (La Gazzetta dello Sport)
Aston Villa na duba yuwuwar gabatar wa Leon Bailey sabon kwantiragi kasancewar kwantiragin matashin ɗan wasan na gaba na gefe ɗan Jamaica zai ƙare a watan Yuni na 2025. (Football Insider)
Arsenal na da ƙwarin gwiwar cimma sabuwar yarjejeniya da ɗan bayanta Ben White ɗan Ingila, wanda yake jin daɗin zama a kungiyar. (Fabrizio Romano)
Ana sa ran Manchester City da West Ham su yi ƙoƙarin sayen matashin ɗan bayan Chelsea Ian Maatsen, mai shekara 21, wanda aka ce Barcelona ma na sha'awarsa, idan har ɗan Holland din bai sabunta zamansa a Old Trafford ba. (Teamtalk)
Everton na son matashin ɗan gaba na gefe na ƙungiyar Corinthians ta Brazil Wesley Gassova, mai shekara 18, amma kuma fa za ta fuskanci gogayya daga wasu kungiyoyin. (Teamtalk)
Matashin ɗan bayan Jamus Malick Thiaw, mai shekara 22, yana son ci gaba da zama a AC Milan duk da sha'awarsa da Real Madrid da kuma West Ham suke yi. (Calcio Mercato)
Borussia Monchengladbach za ta tsawaita kwantiragin matashin ɗan wasanta na tsakiya Manu Kone ɗan Faransa mai shekara 21, da ƙarin shekara ɗaya, domin ta ya kai 2026. (Rheinische Post daga Get German Football News)
Matashin ɗan wasan tsakiya Romeo Latvia na Belgium mai shekara 19, wanda har yanzu bai fara taka wa Chelsea leda ba tun bayan da ta saye shi daga Southampton a bazara, zai sake zaman jira har zuwa watan Nuwamba kafin ya fara wasa saboda raunin da ya ji a lokacin atisaye. (Mail)