Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG da Mbappe za su yi magana ta ƙarshe, Newcastle na son Rowe na Arsenal
Paris St-Germain za ta gabatar wa Kylian Mbappe tayi na ƙarshe na sabunta kwantiraginsa, yayin da Real Madrid ke dakon ganin abin da zai biyo baya. (Sport)
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal da Ingila Emile Smith Rowe, mai shekara 23, ya ɗauki hankalin Newcastle United, inda take nuna sha'awarsa. (Mirror)
Ana danganta Inter Milan da ɗan wasan tsakiya na West Ham Tomas Soucek, ɗan ƙasar Czech da kuma Kelechi Iheanacho, na Najeriya da ke Leicester City. (FC Inter News )
Sai dai kuma West Ham za ta mayar da hankali kan tattaunawa a kan kwantiragi da Soucek, wanda a bazara mai zuwa zai kasance ba shi da ƙungiya. (Football Insider)
Chelsea na shirin sayar da ɗan bayanta na Ingila Trevoh Chalobah, a watan Janairu yayin da zakarun Jamus Bayern Munich ke nuna sha'awarsu a kansa. (Fabrizio Romano daga Goal)
Kociyan ƙasar Girka Gus Poyet ya ce zai so ya zama kociyan Jamhuriyar Ireland a wani lokaci nan gaba, bayan da ya jagoranci Girka ta doke IIreland ɗin karo biyu a wasannin neman gurbin gasar cin kofin ƙasashen Turai ta Euro 2024. (Irish Independent)
Manchester City za ta samu sama da fam miliyan 8, idan har Liverpool ta sayi ɗan wasan gaba na gefe na Bayern Munich da Jamus Leroy Sane, saboda yarjejeniyar tafiyarsa ƙungiyar ta Jamus daga Man City. (Mirror)
Bisa ga dukkan alamu akwai sauran magana a game da yuwuwar sayen hannun jari na kashi 25 cikin ɗari da Jim Ratcliffe zai yi a Manchester United, kuma wataƙila maganar ta yi tsawo sosai. (Independent)
Bayern Munich da Barcelona suna son ɗan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz, mai shekara 20. (Mundo Deportivo)
Manchester United ba ta gaggawar sayar da Scott McTominay, to amma idan ta samu farashi mai kyau za ta yi nazarai a kai. (90min)
Tsohon kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ba zai zama sabon mai horad da Charlotte FC ba bayan da shugaban ƙungiyar Joe LaBue ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara cewa ɗan ƙasar ta Norway yana ziyarar ƙungiyar ta Amurka ne kawai. (Manchester Evening News)