A sifaniya za a tantance tsakanin Bayern Munich da Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich da Real Madrid sun tashi 2-2 a wasan farko a daf da karshe a Champions League ranar Talata.
Vinicius Junior ne ya fara ci wa Real Madrid kwallon a minti na 24 a karawar da suka yi a Allianz Arena.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Bayern Munich ta farke ta hannun Leroy Sane, minti hudu tsakani Harry Kane ya kara na biyu a bugun fenariti.
Sauran minti bakwai a tashi daga karawar Real Madrid ta farke a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Vinicius Junior.
Bayern ta kawo wannan gurbin bayan da ta yi waje da Arsenal, ita kuwa Real Madrid ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Manchester City mai rike da kofin bara.
Real Madrid mai Champions League 14 tana daf da lashe La Liga na bana na 36 jimilla, ita kuwa Bayern Munich mai kofin zakarun Turai shida ta rasa daukar Bundesliga na kakar nan, bayan lashe 11 a jere.
Bayern Leverkusen ce ta dauki babban kofin tamaula na Jamus a karon farko a tarihin kungiyar sama da shekara 100.
Ranar Laraba 8 ga watan Mayu za a buga wasa na biyu a Champions League, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin Bayern Munich a Santiago Bernabeu.











