Arsenal za ta iya raba gari da Partey, ƙungiyoyin turai na rububin Davies

Asalin hoton, Reuters
Arsenal na fuskantar barazanar rasa ɗan wasan tsakiyar Thomas Partey, mai shekara 31, a kan kyauta da bazara. (Mirror)
Wasu manyan ƙungiyoyin Turai da dama sun nuna sha'awarsu kan ɗan wasan baya na Bayern Munich Alphonso Davies ɗan ƙasar Canada mai shekaru 24, ciki har da Liverpool da Real Madrid da kuma Barcelona.
Manchester City ta amince cewa za ta da buƙaci yin cefane a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu sakamakon rashin tagomashi da ta ke fama da shi a halin yanzu. (Telegraph)
City ta nuna sha'awar ɗaukar dan wasan Valencia Pepelu mai shekara 26 domin ya maye gurbin Rodri da ke fama da rauni a halin yanzu. (Estadio Deportivo)
Matashin ɗan wasan gaban Chelsea Carney Chukwuemeka, mai shekara 21, yana jan hankalin wasu ƙungiyoyin gasar Premier. (Football Insider)
Dan wasan gaban Brazil Richarlison, mai shekara 27, ba zai amince da tayi daga tsohon kulob ɗinsa Fluminense ba yayin da yake ƙoƙarin ci gaba da kasancewa a Tottenham.(TNT Sports Brazil)
Spurs na tunanin dawo da ɗan wasan baya na Ingila Ashley Phillips, mai shekara 19, daga zaman aro da ya ke yi a Stoke a watan Janairu don taimakawa wajen magance matsalar rauni da kulob ɗin ke fama da ita. (Standard)
Manchester United za ta yi zawarcin ɗan wasan bayan Girona Miguel Gutierrez, mai shekara 23, a watan Janairu. (TeamTalk)
Tsohon darektan wasanni na Manchester United Dan Ashworth na iya maye gurbin Edu a Arsenal, duk da cewa kulob ɗin na nazari kan Roberto Olabe na Real Sociedad. (Mail)
Crystal Palace na zawarcin ƴan wasa uku daga Lyon, da suka haɗa da ɗan wasan Ghana Ernest Nuamah, mai shekara 21, da ɗan wasan Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21, da kuma ɗan wasan baya na Faransa Sael Kumbedi, mai shekara 19. (TBR Football)
Ɗan wasan bayan Manchester United da Sweden Victor Lindelof, mai shekara 30, yana jan hankalin Ƙungiyoyi da dama a gasar Serie A ciki har da AC Milan. (TeamTalk)











