Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amorim bai yanke shawara kan komawarsa Man U ba
Kocin Sporting Lisbon Ruben Amorim ya ce har yanzu bai yanke shawara kan makomarsa Manchester United ba, bayan ƙungiyar ta nuna sha'awarta ta naɗa shi kocinta.
A ranar Talata ne Sporting ta tabbatar da cewa United ta tuntuɓe ta, kuma ta bayyana shirinta na biyan Amorim Yuro miliyan 10 (£ 8.3m).
Da yake magana bayan nasarar da ƙungiyarsa ta yi kan Nacional da ci 3-1 a wasan kusa da na ƙarshe na gasar cin kofin Portugal ranar Talata, Amorim ya shaidawa manema labarai: "Ba a kammala komai ba tukuna. Ban sani ba ko wannan ne wasan bankwana ko a'a."
Sannan a wani taron manema labarai ya ƙara da cewa: "Manchester United ta nuna sha'awarta, akwai batun kuɗin kwantiragi kuma idan na tabbatar da wasu abubuwa, zan zo nan in bayyana matsayina, domin zaɓina ne."
Amorim ya ƙara da cewa zai ci gaba da gudanar da atisaye da Sporting domin shirya wa wasan da za su kara da Estrela da Amadora ranar Juma'a.
Da aka tambaye shi ko zai kasance a filin wasa na Old Trafford a wasan da Manchester United za ta yi da Chelsea ranar Lahadi, Amorim ya ce: "Zan kasance a nan ne." Amma da aka ƙara yi masa tambayar sai kara da cewa: "Ban sani ba."