Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda rayuwar wasu ta sauya bayan harin 7 ga watan Oktoba a Isra'ila
Batsheva ba ta da masaniyar halin da mijinta ke ciki, yana raye ko ya mutu, shi kuwa Abdullah na shiga shekarun samartaka a matsayin maraya, yayin da Christina da Abdulrahman ke fatan sake tafiya a nan gaba.
Yayin da suke magana daga Gaza da Lebanon da kuma Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, sun shaida wa BBC yadda rayuwarsu ta sauya jim kaɗan bayan hare-haren ranar 7 ga watan Octoban bara.
Aƙalla kusan shekara guda tun bayan da maharan Hamas suka kutsa cikin Isra'ila, inda suka kashe 1,200 tare da garkuwa da mutum 251.
A martani kan hakan, Isra'ila ta ƙaddamar da manyan hare-hare da sama da ƙasa zuwa cikin Gaza, inda aka kashe aƙalla mutum 41,000, kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta bayyana.
‘Ba mu san mummunan abu zai faru da mu ba’
Kwana guda kafin harin 7 ga watan Oktoba, Ohad Yahalomi tare da 'yarsa Yael mai shekara 10 sun fita domin kallon dabbobi a wani wuri da ke kusa da gidansu.
Yayin da ɗayan ɗan nasa, Eitan mai shekara 12, ke wasa da ƙwallo tare da abokansa.
Matar Ohad, Batsheva na gida tare da ƙaramar 'yasu wadda ba ta ƙarasa shekara biyu ba.
Wannan ita ce irin rayuwar da ake yi a Nir Oz kibbutz, wani ɗan ƙaramin gari - mai nisan aƙalla mil guda daga kan iyakar Gaza - da aƙalla mutum 400, ke rayuwa a cikinsa.
“Muna son rayuwa a can muna jin dadin garin. Yadda kasan aljanna a garemu'', in ji Batsheva mai shekara 45.
Da asubahin fari jiniyar na'urorin ankararwa ta tashe su daga barci, wata alama da ta tabbatar musu cewa babu makawa, masu ɗauke da makamai daga Gaza sun kawo musu hari.
Mintuna bayan haka, suka fara jin ƙarar rokoki, da ihun kabbara ''Allahu Akbar''tare da wasu ƙarar harbin bindiga daga wajen gidansu.
Mutanen gidan sun ɗauki sa'o'i maus yawa suna jira a cikin gidansu, cike ɗimuwa da kiɗima da fargabar halin da su shiga. To amma nan da nan 'yan bindigar suka kewaye gidansu suna ƙoƙarin ɓalle ƙofa, Ohad ya fita ɗakin da suke ɓoye, a wani yunƙuri na hana maharan shiga gidan nasa.
“A kowane miti yakan faɗa mana cewa yana sonmu,” in ji Batsheva.
Riƙe da bindigogi ƙirar Kalashnikov sanye da rigunan kariyar gurneti, maharan sun kutsa gidan tare da harbe Ohad, kafin ya gano ɗakin da iyalan ke ɓoye. ''Sun cua mana bindigogi sannan suka riƙa yi mana Turanci suna cewa 'Come to Gaza' (Ku zo Gaza). Nan da nan na fahimci me suke nufi, in ji ta.
An ɗora Batsheva tare da 'ya'yan mata guda biyu, kan babur guda, yayin da aka ɗora Eitan kan wani babur ɗin tare da wani ɗan ƙasar waje, aka yi Gaza da su.
Batsheva da 'ya'yan nata biyu sun kuɓuta bayan da babur ɗin da suke kai ya lalace. To amma an tafi da Eitan tare da mahaifinsa inda aka yi garkuwa da su.
Hamas ta riƙe Eitan a Gaza har tsawon kwana 52. Batsheva ta ce Hamas ta tilasta wa ɗan nata kallon bidiyon da suka naɗa a lokacin harin. ''Ya ga yadda suka yi wa mutane da jarirai da mata kisan gilla,'' in ji ta.
An saki Eitan cikin watan Nuwamba lokacin musayar fursunoni da aka yi bayan fara yaƙin.
Tsagin masu ɗauke da makamai na Falasɗinawa sun fitar da bidiyon Ohad a watan Janairu, inda aka gan shi da raunuka, daga baya kuma suka ce ya mutu a wani hari da Isra'ila ta kai.
Rundunar sojin Isra'ila ta faɗa wa Batsheva cewa ba ta iya tabbatar da iƙirarin ba, sannan ba su iya faɗa musu halin da Ohad ke ciki ba.
Nir Oz na ɗaya daga cikin garuruwan da hare-haren 7 ga watan Oktoba suka fi ƙamari. An kashe gomman mazauna garin tare da garkuwa da wasu. A yanzu garin ya zama kufai yayin da gidaje da dama suka ƙone.
Batsheva ta ce 'ya'yanta na munanan mafarkai, inda suka kwashe kusan shekara guda suna kwana tare a kan gado guda. A koyaushe suna tambayar yaushe mahaifinsu zai dawo.
“Abun baƙin cikin shi ne ba mu san halin da yake ciki ba, ko yana raye ko kuma ya mutu. Ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba''.
'Ina ma a ce na yi shahada'
Abdullah na dab da cika shekara 13 a lokacin da Hamas ta ƙaddamar da hare-haren 7 ga watan Oktoba kan Isra'ila.
Kafin kai harin rayuwarsa a garin al-Tawam da ke arewacin Gaza cike take da farin ciki, inda yake zuwa makaranta da buga wasan ƙwallon ƙafa tare da abokansa da zuwa wuraren shaƙatawa tare da iyayensa da 'yan'uwansa namiji guda da mata biyu.
Kwana guda kafin bikin ranar haihuwarsa, aka riƙa yaɗa takardun gargaɗin barin yankin da suke zuwa kudanci.
Nan take iyalan suka haɗa 'yan komatsansu suka kama hanyar Salah al-Din, wadda sojojin Isra'ila suka ware a matsayin hanyar zuwa tudun mun tsira.
Amma yayin da suke tsada ta tafiya a kan titin, ya ce harin Isra'ila ta sama ta faɗa kan motarsu.
“Kwatsam! sai muka ji iaka ta yi jifa da ni tare da yayana daga cikin motar]], in Abduallah.
A lokacin da abin ya faru yayan nasa mai suna Ahmad shekarunsa 16, Ya gamu da raunin da dole sai da aka yanke masa ƙafa guda, inda a yanzu yake tafiya da ƙafa guda tare da taimakon ƙarfe.
Ɓaraguzan motar da suke ciki ya yanki Abdullah a dantse da kansa da kuma bakinsa. Ya cire rigarsa inda nan ma ya tarar da wasu raunak biyu a cikinsa.
Daga baya ne kuma aka samu gawarwakin mahaifinsa da mahaifiyarsa a ƙone sun yi filla-filla, kamar yadda 'yan'uwansu suka shaida wa BBC.
Abdullah da danginsa da wasu shaidu da dama sun shaida wa BBC cewa jirgi marar matuƙi ne ya harba musu makamai mai linzami.
Sojojin Isra'ila sun musanta kai hare-haren kan jerin gwanon motocin fararen hula a wannan rana, suna masu bayya iƙirarin da cewa ''ƙarya ce maras tushe''.
“Bayan cikakken bincike, mun gano cewa babau wata hujja da ta tabbatar da cewa sojojin Isra'ila sun kai hari a wannan lokaci,'' kamar yadda kakakin runsunar sojin ya shaida wa BBC.
Abdullah na tuna lokacin da likitoci suka riƙa kaucewa tambayar da ya riƙa yi musu kan halin da iyayensa ke ciki, amma a lokacin da 'yan'uwansa da kakarsa suka shaida masa cewa iyayaen nasa sun rasu, ya ce kawai dama tabbatar masa suka yi saboda ''na daɗe da jin hakan a raina'', in ji shi.
“Idan da ace na yi shahada a lokacin, da hakan ya fi min, maimakon ganin abubuwan da ke faruwa a yanzu,'' in ji shi.
A yanzu Abdullah na zaune tare da kakarsa a Khan Younis da ke kudancin Gaza, tare da 'yan'uwansa mata guda biyu, Minna mai shekara 18 da kuma Hala mai shekara 11.
A ranar da aka kashe iyayensa, 'yan'uwan nasa mata na arewacin Gaza saboda ba su samu wuri a motar da ta ɗauko su ba. Shi kuma yayansa Ahmad na Qatar inda yake wata jinya.
“A yanzu dariya da ƙaurace wa fuskokinmu, mun rasa mahaifiyarmu da mahaifimu da kawunmu, daman su ne ke sanya mu farin ciki har mu yi dariyar,'' in ji Abduallah.
Bayan na farka a asibiti na gane na rasa ƙafata ɗaya’
“Koyaushe nakan gabatar da kaina a matsayin 'yarjarida mai ɗaukar hoto. Amma a yau zan iya cewa ni guntun yaƙi ce,'' in ji Christina Assi.
Ta kasa samaun damar komawa ƙasarta ta asali, Lebanon domin kawo rahotoni tare da ɗaukar hotounan yaƙin da ke faruwa a ƙasar a halin yanzu a matsayinta na mai ɗaukar hoto da ke aiki da fitaccen kamfanin dillancin labarai na AFP.
Jim kaɗan bayan hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba, ƙungiyar Hezbollah mai ɗauke da makamai ta Lebanon ta fara kai harin rokoki zuwa cikin Isra'ila, lamarin da ya haifar da hare-haren kan iyaka, wanda daga baya ya faɗaɗa zuwa babban yaƙi.
A ranar 13 ga watan Oktoban bara, Christina tare da wasu 'yan jarida suka je wani ƙauye a kudancin Lebanon, aƙalla kilomita guda daga kan iyakar Isra'ila, wurin da ake musayar hare-haren.
Christina, mai shekara 29, ta ce dukkansu sun sanya riguna da hulunan da ke nuna alamun su 'yan jarida ne, yayain da motar da suke ciki ke ɗauke da rubutun "TV' da alamar kaset mai launin ruwan ɗorawa. Ta ce a tunaninta babu abin da zai same su.
Sai kwatsam! suka fara jin harbi. Abu na gaba da Christina za ta iya tunawa shi ne, tana ƙoƙarin fita daga motar, sai ta ci karo da harbi. Ta faɗi ƙasa tare kyamararta da rigarta mai kariya daga harbi mai nauyin gaske, inda ta riƙa ƙoƙarin guduwa.
''Ina iya ganin ƙafafuna na zubar da jini, kuma ba zan iya tayawa ba,'' in ji ta.
Kwana 12 bayan haka, Christina ta farka a asibiti. “Na tashi sai kuma na fahimci cewa na rasa ƙafa ta guda.”
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar ɗan jaridar Reuters, Issam Abdallah, mai shekara 37, tare da raunata mutum shida.
“A lokacin da ma'aikaciyar jinya ta sanar da ni wanda ya mutu, kawai sai na tuno da shi, na kasa yarda ya mutu” in ji shi.
Wani bincike da Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon suka yi ya ce Isra'ila ta harbo harsasai biyu masu tsayin milimita 120 kan tawagar ''da ta bayyana ƙarara cewa ta 'yan jaridar'' ce, abin da kuma ya saɓa wa dokokin duniya.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun yi kiran gudanar da bincike kan hari a matsayin laifukan yaƙi.
Rundunar sojin Isra'ila ta shaida wa BBC cewa dakarunta sun ɗauka ''yan'taadda ne suka kutso'' cikin Isra'ila a lokacin sannan suka yi amfani da tankokin yaƙi da makaman atilare wajen yin harbi don kare kansu. Ta kuma ƙara da cewa har yanzu suna ci gaba da bincike kan batun.
A yanzu, kusan shekara da faruwar harin, har yanzu Christina na ba ta fara tafiya ba.
A watan Yuli ne ta riƙe wutar gasar Olympic a kan kujerar marasa lafiya, tare da sauran abokan aikinta daga AFP, domin girmama 'yan jaridar da suka raunata da waɗanda aka kashe a faɗin duniya.
Duk da wannan abu da ya faru, tana fatan wata wara ta koma bakin aikinta.
‘Na yi ta ihu amma ba a amsa min ba’
Da wani maraice ne, Abdulrahman Al Ashqar ya ce shi da wani abokinasa mai suna, Laith Shawahneh, na shwagi a kan layin unguwarsu, suna shan sigari bayan shafe tsawon wuni a kasuwan suna sayar da hatsi.
“Kwatsam! sai aka jefa mana bam,” in ji matashin mai shekara 18 wanda ke tuna abin da ya faru ranar 1 ga watan Satumba.
Harin jirgin saman Isra'ila ne ta faɗa wa matasan biyu a ƙauyen Silat al-Harithiya da ke yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye.
Abdulrahman yana tuna ƙarar fashewar roka, amma babu abinda ya yi.
“Taku ɗaya kawai na ƙara,” in ji shi. “Nan take na fara ihu ina kiran Laith, amma bai amsa ba.”
An kashe Laith, mai shekara 16, yayin da Abdulrahman ya samu munanan raunuka, inda ya aka kai ga yanke masa ƙafafunsa guda biyu.
Abdulrahman ya ce bayan kamar kwana 10 da faruwar lamarin, likitoci sun shaida masa cewa sau uku zuciyarsa na daian bugawa.
Kafin harin, Abdulrahman na gudanar da harkokin rayuwarsa na yau da kullum, inda yake farawa da zuwa sallah asuba, sannan karin kumallo tare da abokansa, sanna ya taimaka wa mahaifinsa wanda arkomi ne a kasuwar hatsi ta ƙauyensu.
A yanzu ya dogara ne kan ɗan'uwansa wanda ke taimaka masa wajen gudanar da muhimman abubuwa kamar zuwa ban ɗaki, yayin da mahaifiyarsa ke ba shi abinci.
BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Isra'ila (IDF) don jin ta bakinta. A lokacin harin, IDF ta ce jirgin yaƙinta ya kai harin ne, kuma ya ''faɗa kan 'yan ta'adda jim kaɗan bayan ganinsu suna jefa abun fashewakan dakarunta da ke aiki a yankin Jenin daidai Gadar Menashe''.
Da aka tambaye shi ko yana riƙe da makami ko wane iri, sai ya ce makamai kamar ya? Na fa fita daga gida ne. ''Ina yawo a unguwarmu sanye da fararen tufafi na''
A baya ba shi da burin da ya wuce mallakar mota, ''amma yanzu babban burina shi ne na ganni ina tafiya da ƙafa ta'', in ji shi.
Rahoto daga ma'aikatan sashen Larabci na BBC: Michael Shuval da Haya Al Badarneh da Manal Khalil da Eman Erikat da kuma Alaa Daraghme. Wanda Dima Al Babilie ya shirya