Arsenal ta yi rashin nasara a karon farko da fara kakar nan

An wallafa

Arsenal ta yi rashin nasara a karon farko da fara kakar bana, bayan da Lens ta doke ta 2-1 a wasa na bibiyu a rukuni na biyu a Champions League.

RC Lens ta farke kwallon ta hannun Adrien Thomasson a minti na 25, bayan da Gunners ce ta fara zura kwallo a raga ta hannun Gabriel Jesus a minti na 14 da take leda.

Elye Wahi ne ya kara na biyu bayan da suka yi nisa da komawa zagaye na biyu a fafatawar da suka yi a Faransa ranar Talata..

Daya sakamakon wasan cikin rukuni tsakanin PSV Eindhoven da Sevilla sun tashi 2-2 a Netherlands.

Kenan bayan kammala wasa na bibiyu a cikin rukuni Lens ta koma ta daya da maki hudu, sai Arsenal ta biyu da maki uku da Sevilla mai maki biyu da Eindhoven mai daya tal.

Ranar 23 ga watan Oktoba, Sevilla za ta karbi bakuncin Arsenal a karawa ta uku-uku a cikin rukuni na biyu a Champions League.

A kuma ranar ce PSV Eindhoven za ta ziyarci Lens a Faransa a daya wasan na rukuni na biyu.

Karon farko da aka ci Arsenal a bana a dukkan fafatawa 10 da ta yi da fara kakar bana, wadda ta yi nasara a wasa biyar a Premier da daya a Champions da League Cup da canjaras biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Tun farko Gunners ta fara kakar nan da tashi 1-1 da Manchester City a Wembley daga nan ta dauki Community Shield a bugun fenariti ranar 6 ga watan Agusta.

Kungiyar da ke Emirates tana mataki na uku a kan teburin Premier mai maki 17, yayin da City ce ta daya da maki 18, Tottenham ta biyu mai maki 17.

Ranar Lahadi 8 ga watan Oktoba, Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester City a karawar mako na takwas a Premier League.

Daga nan kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama za ta je gidan Chelsea a wasan Premier ranar 21 ga watan Oktoba karawar mako na tara.

Arsenal za ta ziyarci Sevila a Sifaniya a wasa na uku-uku a cikin rukuni a Champions League ranar 24 ga watan Oktoba.