ECOWAS ta samu goyon bayan kasashen yankin tsakiyar Afrika kan matakin da ta dauka kan Nijar

ECOWAS
Bayanan hoto, ECOWAS
An wallafa

Kungiyar kasashen yankin tsakiyar Afirka, wato Economic Community of Central African States (ECCAS), ta bayyana goyon bayanta ga matakan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ta ECOWAS ta dauka, game da dambarwar siyasar jamhuriyyar Nijar.

Shugaban kungiyar ta ECCAS wanda kuma shi ne shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya isar da wannan sakon, a wata ziyarar aiki da ya kai wa shugaban Najeriya, kuma shugaban ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Ali Bongo Ondimba , ya bayyana cewa kungiyar na goyon bayan ECOWAS dangane da matakan da ta dauka a kan juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyyar Nijar.

Mista Bongo ya jaddada cikakken goyon bayan kungiyar ta ECCAS a kan shawarwarin da ECOWAS ta dauka, kana bin da ya kira ‘‘karbe ragamar shugabanci ta hanyar da ta saba da kundin tsarin Mulki, da sojoji suka yi a jamhuriyyar Nijar’’.

“Matakin na ECOWAS wani tabbaci ne muraran, cewa katsalandan na sojoji ga gwamnatin dimokuradiyya wani al'amari ne da ba za a taba amincewa da shi a ko'ina ba, kuma batu ne da tuni ya zama tsohon yayi a nahiyar Afirka”, in ji shi.

Shugaban na kasar Gabon, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar ta ECCAS, ya yi alkawarin isar da sakon kwakkwaran hadin kan da ke tsakanin kungiyoyin yankunan biyu na Afirka, ga shugabannin gwamnatin soja ta Nijar, a taron da ya ce zai yi da su nan da 'yan kwanaki masu zuwa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, kuma shugaban kungiyar ta ECOWAS dai, ya bayyana farin ciki tare da jinjina, game da goyon bayan da kungiyarsa ta samu daga takwararta ta ECCAS, kan dambarwar siyasar da ta dabaibaye jamhuriyyar Nijar.

A baya baya nan ne Shugabannin ƙasashen Ecowas suka ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar, su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin sojoji na ranar 26 ga watan Yuli.

Sai dai ba su samar da takamamen lokacin amfani da karfi ba wanda suka ce shi ne "zabi na karshe" idan dukannin matakan diflomasiyya da na siyasa suka gaza.

A ranakun Alhamis da Juma'a shugabannin tsaro na yankin za su yi taro a birnin Accra na kasar Ghana a kan yadda za a shawo kan rikicin.

Juyin mulkin soja ya ja hankalin duniya inda gwamnatocin kasashen ketare da dama ke yin kira da a warware rikicin cikin lumana.