Ivory Coast ta lashe kofin Afirka bayan cin Najeriya

An wallafa

Ivory Coast ta lashe kofin Afirka na bana, bayan cin Najeriya 2-1 a wasan karshe ranar Lahadi.

Ivory Coast ce ta karbi bakuncin gasa ta 34 a babban wasannin tamaula na Afirka, wadda ta lashe kofin karo na uku a tarihi.

Super Eagles ce ta fara cin kwallo ta hannu William Troost-Ekong saura minti takwas su je hutun rabin lokaci.

Franck Kessie ne ya farke kwallo daga bugun kwana da Adingra ya buga, hakan ya sa wasan ya koma 1-1.

Saura minti tara a tashi daga wasan na hamayya ne Sebastien Haller ya ci wa Ivory Coast kwallo na biyu da ya bai wa kasar damar daukar Afcon 2023.

Mai masukin baki ta samu wannan nasarar duk da korar kociyanta Jean-Louis Gasset, bayan rashin nasara a wasa biyu a rukunin farko.

Ivory Coast ta fara da cin Guinea Bissau 2-1, sai Najeriya ta yi nasara a kanta da cin 1-0 da kuma Equatorial Guinea ta dura mata 4-0.

Hakan ya sa Equatorial Guinea da Najeriya suka hada maki bakwai-bakwai kowacce da kuma Ivory Coast ta ukun teburi.

An kuma zabi mai masukin baki a cikin hudun da suka cike gurbin zagaye na biyu a matakin wadanda suka taka rawar gani a fafatawar rukuni.

Daga nan Ivory Coast ta fitar da mai rike da kofin bara, Senegal a zagaye na biyu, sannan ta cire Mali a kwata-fainals da kai wa wasan karshe bayan cin DR Congo.

Tun farko tawagar ta lashe Afcon a 1992 da kuma 2015 ta kuma zama ta farko da ta karbi bakuncin wasannin, sannan ta lashe kofin, bayan bajintar Masar a 2006.

Kociyan riƙon kwarya, Emeerse Fae shi ne ya ja ragamar zuwa wannan namijin korin a gasar kofin Afirka a bana.

Ivory Coast ta kashe $1bn (£0.79bn) wajen karbar bakuncin gasar da ya hada da gina wurare da bunkasa filayen kasar, inda shugaban kasa, Alassane Outtara ya halarci wasan karshe a filin da aka sa sunansa.

Tawagar da ake kira The Elephants za ta karbi ladan $7m (£5.54m) yayin da Najeriya, wadda ta yi ta biyu za ta karbi $4m daga hukumar kwallon Afirka.

Ivory Coast ta zama ta 12 da ta shirya Afcon ta kuma lashe kofin, Super Eagles tana da kofin uku, wadda wasan karshe ne ta yi nasara a gabaki dayan wasannin da aka yi a Afcon.

Super EEagles ta fara da yin 1-1 da Equatorial Guine, sannan ta ci Ivory Coast 1-0 da yin nasara a kan Guniea Bissau 1-0 a karawar cikin rukunin farko.

Najeriya ta doke Kamaru 2-0 a zagaye na biyu da cin Angola 1-0 a daf da na kusa da na karshe, sannan ta yi nasara a kan Afirka ta Kudu a bugun fenariti 4-2, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.

Kasar Morocco ce za ta karbi bakuncin wasannin Afcon a 2025 da za a gudanar da gasa ta 35.