Har yanzu Saka da Martinelli na jinya

Asalin hoton, Getty Images
Bukayo Saka da Gabriel Martinelli na ci gaba da jinya, ba su samu halartar atisayen Arsenal ba ranar Litinin a Netherlands.
Gunners na shirin buga wasan zagayen farko na ƴan 16 a Champions League da za ta fafata a gidan PSV Eindhoven ranar Talata.
Sauran ƴan wasan Gunners da ke jinya sun haɗa da Kai Havertz da Gabriel Jesus da kuma Takehiro Tomiyasu.
To sai dai ana sa ran Saka da Martinelli na daf da komawa atisaye bayan jinya, ana cewa a cikin watan Maris Saka zai fara atisaye, Martinelli zai riga Saka komawa motsa jiki.
Saka wanda ya buga karawa 24 a dukkan fafatawa a bana, ya ji rauni a wasan da Arsenal ta je ta ɗura 5-1 a Crystal Palace a Premier League ranar 21 ga watan Disamba.
Shi kuwa Martinelli, wanda ya yi wasa 35 a dukkan karawa ya ji rauni a League Cup da Newcastle ta yi waje da Arsenal ranar 5 ga watan Fabrairu a St James's Park.
PSV Eindhoven da Arsenal za su fafata karo na 11 a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, Arsenal ta yi nasara huɗu da canjaras huɗu, PSV ta ci biyu daga ciki.
Wasa na karshe da suka fuskanci juna a tsakaninsu shi ne a Champions League a kakar 2023/24.
Champions League ranar Talata 12 ga watan Disambar 2023
- PSV Eindhoven 1 - 1 Arsenal
Champions League ranar Laraba 20 ga watan Satumbar 2023
- Arsenal 4 - 0 PSV Eindhoven
Arsenal tana ta biyu a teburin Premier League da maki 54 bayan wasan mako na 27, wadda ta ci karawa 15 da canjaras tara aka doke ta wasa uku a kakar nan.









