Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool ta ɗare teburin Champions League bayan cin Real Madrid
Liverpool ta doke Real Madrid 2-0 a wasa na biyar-biyar a Champions League da suka kara a Anfield ranar Laraba.
Ƙungiyoyin sun yi hutu ba ci, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Liverpool ta zura biyu a raga ta hannun Mac Allister da kuma Gakpo.
Wannan shi ne wasa na 12 a tsakaninsu a gasar ta zakarun Turai, inda Liverpool ta yi nasara ta huɗu da canjaras ɗaya, Real Madrid ta ci karawa bakwai.
Ƙungiyoyin sun fara fuskantar juna ranar Laraba 27 ga watan Mayun 1981 a European Cup, inda Liverpool ta yi nasara 1-0.
Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta ɗaya a kan teburin gasar zakarun Turai ta bana da maki 15, bayan da ta lashe dukkan wasa biyar da ta yi.
Real Madrid mai riƙe da kofin bara kuma na 15 jimilla, tana ta 24 a kan teburin da maki shida, sakamakon da ta yi nasara biyu daga wasa biyar a kakar nan.
Liverpool tana da Champions League shida, kuma na ƙarshe da ta lashe shi ne a 2018/19 tare da Jurgen Kloop.
Ƴan wasan da Carlo Ancelotti ya je da su Anfield ranar Laraba.
Ƴan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fran González.
Masu tsare baya: Lucas Vázquez, Vallejo, Fran García, Rüdiger, Mendy da kuma Asencio.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Arda Güler da kuma Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Mbappé, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.
Wasa 12 da aka buga tsakanin Liverpool da Real Madrid
Champions League Laraba 27 ga watan Nuwamba 2024
- Liverpool 2 - 0 Real Madrid
Champions League Laraba 15 ga watan Maris 2023
- Real Madrid 1 - 0 Liverpool
Champions League Talata 221 ga watan Fabrairu 2023
- Liverpool 2 - 5 Real Madrid
Champions League Asabar 28 ga watan Mayu 2022
- Liverpool 0 - 1 Real Madrid
Champions League Laraba 14 ga watan Afirilu 2021
- Liverpool 0 - 0 Real Madrid
Champions League Talata 6 ga watan Afirilu 2021
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
Champions League Asabar 26 ga watan Mayu 2018
- Real Madrid 3 - 1 Liverpool
Champions League Talata 4 ga watan Nuwamba 2014
- Real Madrid 1 - 0 Liverpool
Champions League Laraba 22 ga watan Oktoba 2014
- Liverpool 0 - 3 Real Madrid
Champions League Talata 10 ga watan Maris 2009
- Liverpool 4 - 0 Real Madrid
Champions League Laraba 25 ga watan Fabrairu 2009
- Real Madrid 0 - 1 Liverpool
European Cup Laraba 27 ga watan Mayu 1981
- Liverpool 1 - 0 Real Madrid