Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ta ci wasan La Liga na biyar a jere da fara kakar bana
Barcelona ta je ta doke Girona 4-1 a wasan mako na biyar a La Liga da suka kara ranar Lahadi.
Lamine Yamal ne ya fara cin ƙwallo a minti na 30, sannan ya kara na biyu minti bakwai tsakani daga baya Dani Olmo da kuma Pedri kowanne ya ci ɗaya.
Saura minti 10 a tashi daga wasan Girona ta zare ƙwallo ɗaya ta hannun Cristhian Stuani.
Kawo yanzu Barcelona ta zura ƙwallo 17 a raga, yayin da huɗu suka shiga ragarta a wasa biyar da fara kakar bana ta La Liga.
To sai dai Barcelona ta kammala karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Ferran Torres jan kati saura minti huɗu a tashi daga fafatawar.
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a kan teburi da maki 15, ita kaɗai ce da ta lashe dukkan karawa biyar da fara kakar nan.
Ta fara zuwa ta doke Valencia 2-1 a wasan makon farko da fara La Liga ranar Asabar 17 ga watan Agusta, sannan ta ci Athletic Bilbao 2-1 a gida ranar 24 ga watan Agusta.
Daga nan Barcelona ta je ta ci Real Valladolid 2-1 a karawar mako na uku ranar 27 ga watan Agusta, sannan ta ɗura 7-0 a ragar Valladolid ranar 31 ga watan Agusta.
Barcelona za ta je Monaco, domin buga wasan farko a cikin rukuni a Champions League ranar Alhamis 19 ga watan Satumba.
Daga nan Villareal ta yi wa Barcelona masauki a wasan mako na shida a La Liga ranar Lahadi 22 ga watan Satumba.
Ita kuwa Girona za ta je gidan Paris St Germain a karawar farko a cikin rukuni a Champions League da za su kece raini ranar Laraba 18 ga watan Satumba.
Haka kuma Valencia za ta karɓi bakuncin Girona a wasan mako na shida a La Liga ranar Asabar 21 ga watan Satumba.