Yadda Yahudawa ke tatsar maniyyin matasan da suka mutu domin samun jikoki

    • Marubuci, Michael Shuval
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
    • Marubuci, Aisha Khairallah
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
    • Aiko rahoto daga, London
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

A Isra'ila ana ta samun ƙarin iyayen da ƴaƴansu suka mutu, suna neman a tatso maniyyin ƴaƴan, waɗanda yawancinsu sojoji ne, a adana shi.

A sassauta wasu daga cikin dokokin yin hakan bayan Harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba, to amma har yanzu wasu iyaye ko iyalan na fushi da nuna ɓacin rai a kan tsawon lokaci ga sharuɗɗan dokoki da za su cika kan yadda za a yi amfani da maniyyin.

Avi Harush ya ci ya ji a jikinsa cewa wani abu mummuna zai faru a cikin kwaki, kafin shugabannin soji su ƙwanƙwasa masa ƙofa.

Murayrsa tana rawa a lokacin da yake bayar da bayanin yadda ya ji lokacin da aka sheda masa cewa ɗansa mai shekara 20, Reef ya mutu a fagen daga ranar 6 ga watan Afirilu na 2024 a kudancin Zirin Gaza.

Haka kuma yana cikin wani lokaci na bayyana matsayarsa, domin an ce masa, Reef na cikin lokacin da za a iya tatsar maniyyinsa. ''Sun tambaye ni ko ina son hakan,'' in ji shi.

Avi ya shaida musu cewa, ba makawa zai so hakan domin ɗansa Reef ya kasance mai son yara, kuma ya so samun nashi na cikinsa.

Reef ba shi da mata ko ma budurwa. To amma da mahaifinsa Avi ya fara yaɗa labarin ɗan nasa , mata da dama sun tuntuɓe shi inda suka yarda a sanya musu maniyyin ɗan domin su haifar wa Reef ɗa.

Ya ce, wannan ya ba su ƙwarin gwiwa da kuma wata madogara, wadda yanzu ta zama babban abin da ya sanya a gaba.

Iyalan na daga cikin ƙarin iyayen da ake ta samu da suka adana maniyyin ƴaƴansu tun bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai kan Isra'ila, inda ta kashe kusan mutum 1,200 tare da garkuwa da 251.

Daga nan Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa sama da 39,000, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana. Haka kuma an kashe Yahudawa kusan 400 a yaƙin.

Tun harin 7 ga watan Oktoba an tatsi maniyyi daga kusan maza matasa 170, - fararen hula da kuma sojoji, a cewar ma'aikatar lafiya ta Isra'ila.

Wannan kusan ya ninka alƙaluman da ake da su sau 15 idan aka kwatanta da shekarun baya.

Hanyar da ake yin wannan kuwa ita ce, ana ɗan yanka marena ne a cire wata ƴar fata, wadda daga jikinta ne za a iya samun maniyyin sai a adana shi ta hanyar daskararwa.

Yawanci ana samun nasarar tatsar maniyyin ne idan an yi hakan cikin sa'a 24 da mutuwar mutum, kodayake kwayoyin za su iya zama da rai har tsawon sa'a 72.

Wasu ƙasashen da suka haɗa da Faransa da Jamus da Sweden sun haramta hakan gaba-ɗaya.

Amma kuma wasu sun sanya dokoki masu tsauri da suka danganci amincewar mutumin kafin rasuwarsa.

A watan Oktoba ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta yi sassauci ga iyaye ta yadda za su iya samun izinin kotu don a yi musu.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta dage, wajen yin hakan ga iyayen da aka kashe ƴaƴansu a shekarun nan.

Yayin da ya kasance cewa akwai sauƙi wajen adana maniyyi wata matsala kuma ita ce ta batu na dokoki na shari'a.

Matan da mazansu suka mutu ko iyayen da ƴaƴansu suka mutu kuma suke soon amfani da maniyyin wanda ya mutun domin haihuwa dole sai sun gamsr da kotu cewa wanda ya mutun yana son haihuwa kafin ya mutu.

Matakin zai iya daukar shekaru musamman ga iyayen da ƴaƴansu suka mutu.

Iyayen da a Isra'ila suka fara adana maniyyin ɗansu suka kuma yi amfani da shi wajen samar da ɗa, su ne Rachel ad Yaakov Cohen, waɗanda wani Bafalasɗine ya harbe ɗansu Keivan, in ji rununar sojin Isra'ila a 2002 a Gaza.

Jikarsu da aka haifa daga wannana maniyyin, Osher – yanzu shekararta 10.

Rachel ta bayyana lokacin da ji labarin mutuwar Keivan- ta rika jin kamar yana kusa da ita: “Na je akwakun kayansa. Ina son na ji ƙanshinsa. Hatta takalmansa sai da na shinshina,” ta ce.

“Hotonsa ya yi min magana. Ya gaya min cewa na tabbatar ya samu ƴaƴa.”

Rachel ya ce sun fuskanci adawa sosai, da mutane da yawa waɗanda ba su fahimci abin da suke so su yi ba ko kuma ba sa goyon bayan abin da suke neman yi”.

Amma jajircewarta a karshe ta kai ga samun gagarumar nasara a fannin shari'a, wadda daga nan ta sanya talla a jarida take neman matar da za ta yarda a sanya mata maniyyin ɗan nasu domin ta samu ciki a haifar musu jika.

Irit – wadda ba ta bayyana sunan mahaifinta ba domin kare sirrinsu, na daga cikin matan da suka amnsa kiran.

Ba ta da aure. Ta ce bayan da ƙwararren masanin halayyar ɗan'Adam da kuma wani jami'in kula da jin daɗin jama'a suka yi nazari a kanta, tare da amincewar kotu, daga nan sai aka dasa mata maniyyin ta fara goyon ciki.

“Wasu mutanen sun ce wai muna wasa da Allah. To amma ni ba na ganin haka,” ta ce.

Ta ƙara da cewa, “Akwai bambanci tsakanin ɗan da ya san mahaifinsa da kuma wanda aka dasa wa mace maniyyin mahaifin.''

Osher ta san cewa an kashe mahaifinta ne a soja. An ƙawata ɗakinta da hotunan kifi (dolphins). Ta ce ta san mahaifinta yana sonsu.

Ta ƙara da cewa, “Na san sun tatsi maniyynsa ne suka nemi uwar da ta dace domin a haife ni.”

“Tatso maniyyi daga ɗanka da ya rasu na da mma'ana sosai,” n ji Dr Itai Gat, darektan rumbun adana maniyyin a asibitin Shamir Medical Center – wanda shi kansa yake yin wannan tiyata ta tatso maniyyin.

Ya ƙara da cewa: “Dama ce ta ƙarshe adana damar haihuwa a nan gaba.”

Ya ce a yanzu an samu sauyi sosai a tsakanin al'umma, inda yanzu da yawa suka yarda da tsarin, to amma dokokin da ake da su a yanzu sun kasance cikas ga mazan da ba su da aure ko abokan mu'amulla ta aure.

Ga irin waɗannan mazan babu wata sheda ta zahiri ta amincewar a yi amfani da maniyyin nasu. Wannan ya sa iyaye da dama da suke cikin jimamin rasa ƴaƴansu a yanayi mai wuya, inda ga maniyyin an adana amma ba za su iya amfani da shi a haihu ba.

Ya ce, “ Ba wai kamar bai wa wani zuciya ko ƙoda ba ne domin cetar rayuwar wani. Muna tattaunawa ne kan haihuwa, samar da yaro ko yarinya - da muka san zai kasance maraya -ba shi da uba.

A yawancin wannan abu, wanda ya mutu ba zai san mahaifiyar yaron da aka sanya wa maniyyinsa ba, kuma duk hukuncin da ya shafi yaron, iliminsa da rayuwarsa wanna uwar ce za ta yanke.

Dr Gat ya ce a da yana dawa da tsarin adana maniyyyin, sai dai idan da izinin mutumin kafin ya mutu, to amma ya ce a yanzu ra'ayinsa ya sauya sakamakoniyayen da ya haɗu da su da suka rasa ƴaƴansu maza a yaƙin da ake yi.

“Na ga yadda abin yake da amfani garesu, yadda a wani lokaci yake sa su jin daɗi,”

Fitaccen malamin addinin Yahudawa Yuval Sherlo, wanda shi ne shugaban cibiyar Yahudanci ta Tzohar Center for Jewish Ethics a Tel Aviv, ya ce batun yana da sarƙaƙiya.

Ya ce, “Bisa tsari ba ma tilasta wa namiji ya zama uba ba tare da amincewarsa ba ko da bayan mutuwarsa.”

Ya ƙara bayani da cewa akwai kuma wasu muhimman manufofi biyu a dokokin Yahudanci - ciyar da salsalar mutum gaba da kuma binne jikinsa gaba ɗaya.

Wasu malaman Yahudawa sun ce ciyar da salsalar gaba, na da muhimmanci saboda haka yanka jikin da ake yi ba matsala, ya ce yayin da wasu kuma ke cewa bai ma kamata a yi abin ba gabaɗaya.

Dokokin da ake amfani da su yanzu a kan batun tsare-tsare ne da babban lauyan gwamnati ya wallafa a shekarar 2003 amma a kundin dokokin ƙasar suke ba.

'Yan majalisar dokokin Isra'ila sun yi yunƙurin fitar da wani ƙudurin doka da zai fayyace dokokin tsarin ƙarara amma kuma haƙarsu ba ta cimma ruwa ba zuwa yanzu.

Mutanen da suke da kusanci da yin dokar sun sheda wa BBC cewa akwai taƙaddama a kan batun samun amincewa ƙarara ta wanda ya mutun, da kuma cewa ko ɗan da aka haifa zai samu haƙƙoƙin da ake ba wa ƴaƴan sojojin da aka kashe a bakin aiki.

Kafofin yaɗa labaran Isra'ila ma sun bayar da rahoto a kan saɓani game da abin da zai faru idan matar marigayin ba ta son yin amfani da maniyyin ta haihu, inda wasu ke adawa da cewa iyayensa sai su karɓe iko da maniyyin su nemi wata matar da za ta yarda a sa mata ta haihu.

Waɗanda suka riga suka adana maniyyin ƴaƴansu suna fargaba cewa idan aka amince doka a kan tsarin a ƙarshe, za ta yi maganin matsalolin amincewa ne amma ba kare doguwar dambarwa ta shari'a ba.

Amma ga Avi, yana cike da ƙwarin gwiwa a halin da yake ciki na damuwa.

Ya nuna min kwali cike da kundin hotuna da littattafai na bayanan rayuwar yau da kullum da abubuwa na tunawa na ɗansa.

Ya ce ba zai gajiya ba har sai ya samar wa ɗansa, Reef haihuwa: ''Za ta tabbata....kuma ƴaƴansa za su karɓi wannan kwalin da ke cike da waɗannan abubuwa.''