Gakpo zai iya buga wasan Liverpool da Toulouse

Cody Gakpo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce ɗan wasan gaba na Liverpool Cody Gakpo, zai buga wasan da ƙungiyarsa za ta yi da Toulouse a gasar cin kofin Europa a ranar Alhamis.

Ɗan wasan mai shekaru 24 ya ji rauni gwiwarsa a wasan da Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Tottenham a watan jiya.

Liverpool ce ta ɗaya a rukunin E bayan ta doke LASK da Union Saint-Gilloise.

Amma Andy Robertson da Thiago Alcantara da Stefan Bajcetic duk ba za su samu damar karawa da Toulouse a Anfield ba.

Klopp ya ce an yi wa Robertson tiyata a kafaɗarsa, yayin da Thiago da Bajcetic ba su fara atisaye tare da sauran abokan wasansu ba.

Abokan hamayyar Liverpool, Toulouse sun ɗauki kofin Faransa a kakar wasan da ta wuce - babban kofinsu na farko - amma sun samu nasara a wasanni uku ne kacal cikin 11 da suka buga a kakar wasanni ta bana.