Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Asensio ya koma Aston Villa domin buga wasannin aro
Aston Villa ta kammala ɗaukar aron ɗan wasan tawagar Sifaniya, Marco Asensio daga Paris St-Germain, kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.
Wanda ya lashe Champions League uku a Real Madrid, shi ne na huɗu da Villa ta dauka a Janairun nan, bayan Marcus Rashford da Donyell Malen da kuma Andres Garcia.
Villa za ta biya albashin ɗan ƙwallon mai shekara 29, amma ba batun sayar da shi, kenan da zarar an kammala kakar nan zai koma Faransa.
Asensio ya ci ƙwallo bakwai a wasa 47 a PSG, tun bayan da ya koma Faransa da taka leda daga Real Madrid a kakar 2023.
Ya taimakawa PSG ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Faransa a bara, sai dai wasa takwas ya yi a bana.
Yana cikin ƴan wasan tawagar Sifaniya da suka lashe Nations League a 2023.