Man United ta tashi 2-2 da Tottenham a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Tottenham sun tashi 2-2 a wasan Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
Rasmus Hojlund ne ya fara ci wa Man United kwallo a minti na uku da take leda, na biyu kenan da ya zura a raga a ƙungiyar ta Old Trafford.
To sai dai a minti na 19 ne Tottenham ta farke ta hannun Richarlison, wanda tun bayan da ya kammala jinya yake cin kwallaye.
Kenan Tottenham ta ci kwallo a karawa 33 a Premier League tun bayan 1-0 da Wolverhampton ta doke ta a Maris din bara.
Saura minti hudu su je hutu ne Man United ta kara na biyu ta hannun Marcus Rashford, haka suka je hutu, kungiyar Old Trafford tana cin 2-1.
Wannan shi ne karon farko da Rashford ya ci kwallo a Old Trafford a dukkan fafatawa a wasa na 14 a bana, wanda ya buga kwallo sau 32 yana nufar raga.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Tottenham ta farke ta hannun Rodrigo Bentancur.
Ranar 19 ga watan Agusta Tottenham ta ci Man United 2-0 a Premier League, inda Pape Sarr ya fara ci mata kwallo daga baya Lisandro Martinez ya ci gida.
Man United za ta buga wasan gaba a FA Cup ranar 28 ga watan Janairu da wata kungiya da za a bayyana a karawar zagaye na hudu.
Sannan kungiyar Old Trafford ta je ta kara da Wolverhampton a gasar Premier League ranar1 ga watan Fabrairun 2024.









