Sadaukarwar mata da ke karɓar albashi mafi karancin a 2022

An wallafa

Mata masu yawan gaske da suke daukar albashi mafi karanci ko kusancin hakan a faɗin duniya, a wannan shekarar sun hakura da abubuwan da za su iya saya watanni 12 da suka gabata, saboda yadda rayuwar take ci gaba da tsada.

Mun zanta da mata daga kasashe guda hudu da suke gudanar da rayuwa ba tare da abubuwan da suke rainawa a da ba – wasu kuma abubuwan da suke shigo musu ya yi ainihin karuwa, suna gode wa sauyin tsari da aka samu a karamar hukuma.

Sabulun wanka da wanki da ake yin shi a gida

Jussara Becello da ke Rio de Janeiro ta ce da ta dawo daga tafiyar sayen kayayyaki da ta saba yi, kayayyakin da ta sayo ba su wuce rabin Jakarta ba, idan aka kwatanta da yadda jakar take cika har ta batse a shekarar da ta gabata.

Kayayyakin da suka shafi wanka da wanke-wanke da wanki, su ta fi mayar da hankali a gare su wajen tattali, kuma ruwan sabulu na wanke-wanke, abu ne da ta daina saye gaba ɗayansa.

A maimakon haka, ta daina watsar da man tuya da ta gama amfani da shi, ta koma tana ba wata makwabciya da take mayar da shi sabulu.

"Nakan yi tuya da soye-soye da mai, idan ya zama ba zan iya ci gaba da amfani da shi ba, sai in ɗura shi a kwalba ta roba in ba wata kawata, nan a makwabtanmu, domin yin sabulu da shi," a cewarta.

  • Mafi karancin albashi: Kudin Birazil 1,212 ($225) a duk wata
  • Rabon da ayi karin albashi: Disamba 2021 (Kashi 10 cikin kashi 100)
  • Tsadar kayayyaki na shekara-shekara kashi 5.9 cikin kashi 100) a watan Nuwamba na 2022

Makwabciyar ta koyi wannan dabara ce a lokacin da take aiki a kamfanin da yake mayar da bola ta zama jari.

Man da aka yi 'yan soye-soye da 'yan toye-toye, su dankali ko kaji, ana gauraya shi da giya, da gishirin da ake kira soda, da kanshi da ake sayoya a kasuwa.

"Tana gauraya shit a yadda warin gishirin sodan da yake da karfin gaske, zai bace" in ji Jussara.

Jussara tana samun albashi mafi karanci na kudin Brazil 1,212 ($225) a duk wata, ban da karo-karonta na fansho, a matsayin mai shara da girki a kamfanin injiniyanci.

A shekarar da ta gabata, tana iya zuwa sinima tare da karamin kaninta, kuma takan tafi da abinci a cikin jakarta da take riketa a hannu domin ba da sadakan abincin ga mutanen da suke kwana a titi.

Amma yanzun ba dama, ta ce "A yanzun, idan na taimaki wani, zan zama ina hana wa kaina abincin da nake bukata a gida.

Nika masara domin samun hatsi.

Wata bakwai ke nan da wata malamar makaranta a Najeriya Rebecca Ogbonna ba ta iya ciyar da 'ya'yanta abin karin kumallon da suka fi so.

An kiyasata cewa a watan Oktoba kayan abinci sun yi tsada sosai da kashi 23 cikin 100 a shekarar.

"Abubuwan da na saba saya da Naira 1,000 ($2.25), a yanzun Naira 3,000 ne ko fiye da haka" In ji Rebecca.

Hakan na nufin Golden Morn, abin da ake dama shi nan take, da kamfanin Nestle yake yi da masara, da 'ya'yanta hudu sukan karya da shi kullum kafin su tafi makaranta, yanzun Rebecca tana yin nata ne da kanta.

"Sai in samu masara da wake, sai in nika su, ko in jika su a ruwa, in bar shi a gida," in ji ta.

  • Mafi karancin albashi : Naira 30,000 ($70) a duk wata, kodayake ya fi haka a wasu jihohin.
  • Kari na karshe 2019
  • Hauhawar farashi: kashi 21.5 cikin kashi 100 a watan Nuwamba na 2022

Sabon abin Karin kumallon bai samu karbuwa ba a wajen yaranta.

"A lokacin da na fara sai suka fara nuna: 'Ni ba na son wannan, ba zan kara shan wannan ba.' Amma ya suka iya dole su ci," in ji Rebecca.

Ita malamar makaranta ce da take samun ɗaya da rabin albashi mafi karanci na Najeriya- Naira 45,000 ($100) – sai dai kudin ba sa isa wajen tallafa wa iyalanta, in ji ta.

"Kafin karshen watan na karar da komai."

Kasa sayen sabbin kayan sawa

A shekarar da ta gataba, Recome tana iya dogara da £9.50 ($11.50) da take samu a duk sa'a guda a matsayinta, ta mai shara a wani gidan ajiye kayayyaki na saidawa ta intanet da ke Landan, amma a yanzun tana fama, duk da tana aiki na karin wasu sa'o'i.

"Saboda ba su da isassun ma'aikata da za su musu aiki, sun ninka mun lokacin aikina kuma haka na amince. Saboda komai ya kara tsada, "in ji matar mai shekara 56 daga kasar Ecuador.

"Nakan yi sa'a 15 zuwa 6 a rana ka san kuwa akwai gajiya."

Hutawa daga wancan aiki shi ma ba abu ne mai sauki ba, saboda ba za ta iya sayen sabuwar katifa domin maye gurbin wacce take sa mata ciwon baya ba.

"Har zuwa shekarar da ta gabata ina iya karbar bashin katifar na biya a hankali, amma a yanzun ina aiki ne domin biyan kudin haya da sayen kayan abinci kawai, babu abin da yake ragewa," kamar yadda take cewa.

  • Albashi mafi karanci: £9.50 ($11.30), a duk sa'a
  • Karin albashi na karshe: Afrilu 2022 (6.6%),
  • Hauhawar farashi: Kashi 9.7% a Nuwamba 2022

Wannan har ila yau yana nufin ta iya sayen sababbin kayan sawa kuma sannu a hankali tana rabuwa da tsofaffin kayan da take da su.

An sha kwantar da ita a sashin kulawar gaggawa a asibiti saboda gajiyar da ke yi mata yawa.

"Sun ba ni shawarar in canza wajen aiki, sai dai ba abu ne mai sauki ba ga wacce ta kai shekaru na".

Babu tikitin zuwa gida don bikin zagayowar ranar haihuwa

Sadaukarwa da wata mata mai shekara 29 Da Woon leong da ke aiki a shaguna sayar da kaya ta hakura da shi, shi ne ziyarar da ta saba kaiwa iyayenta.

Kudin hawa motar bas da na jirgin kasa daga babban birnin Seoul, inda take zaune a yanzu, ya kai kudin kasar 150,000 ($115) kuma a shekarar da ta gabata ya fi karfinta, ba za ta iya biya ba.

"Ina so in kasance tare da su a ranaku farin ciki na, kamar na ranar bikin zagayowar ranar haihuwarsu da tawa.

Abin na matukar damuna musamman a wannan lokaci da kwata-kwata ba zan iya zuwa ba, a cewarta.

Kudaden da take ware wa domin bukatunta yau da kullum ma sun gaggara, saboda tashin farashin kayayyakin abinci, da kuma karin kudin ruwa na banki.

Idan ta karbi rancen kudi domin ajiyewa don gudanar da wata sabga tata, kudin da za ta dinga mayarwa banki sun karu sosa.

  • Albashi mafi karanci: won 9,160 ($6.80) a duk sa'a guda
  • Karin albashi na karshe: Janairu 2022 (5%),
  • Hauhawan farashi: ya karu da kashi 5 a watan Nuwamban 2022

"A yanzu ina yin aiki ne kawai don ba ni da zabi" a cewarta.

"A da nakan iya tara kuɗi domin kai wa iyayena, amma a wannan shekarar na kashe dukkan kudaden da na adana saboda lalurori na gaggawa da kuma kula da su."

Gwamnati ta kara yawan albashin mafi karanci da kashi 5 cikin 100 inda yanzu ya kai won 9,160 ($7.00) a duk sa'a guda a 2022, sai dai kamar yadda ta ce farashin kayayyaki suna ta hauhawa babu kama hannun yaro.

"Ya kamata gwamnati ta kara wa masu karfi haraji domin taimaka wa marasa hali."

Kara kukewa da aiki domin samun karin kudade

Farbani Chhura, mai shekara 40, tana samun rupee 333 (($4) a kullum a inda take yin aiki.

Shi ne albashi mafi karanci ga ma'aikacin gona da ba shi da wata kwarewa.

Tana zaune a jihar Odisha da take arewa maso gabashin Indiya.

Wannan ba wani kudi ne na a zo a gani ba. Sai dai ita da maigidanta suna da akalla, tabbacin suna da aikin yi a kowanne lokaci.

Farbani ta amfana ne da wata doka ta tabbacin samun aiki a yankunan karkara ta kasa ta Mahatma Gandhi, wacce take tabbatar da wadanda suka yi rajistar kwana 100 ta aiki a duk shekara.

Sai dai a kokarin tabbatar da an rage hijira daga yankin da take zaune, gwamnatin jihar Odisha ta kara zuwa kwana 200 a shekarar 2020 da kuma kwana 300 a watan Yuli na shekarar 2022.

A fadin kasar an ba da rahoton cewa mutum miliyan 100 ne ke aiki a karkashin wannan tsari.

A Odisha a wasu sassan gundumomi 4, ciki har da gundumar Balangir inda Farbani take da zama, a yanzun haka suna da tabbacin aiki na kwana 300.

  • Albashi mafi karanci: A Odisha, rupee 333 ($4) a kullum ga ma`aikacin da ba shi da wata kwarewa.
  • Kari albashi na karshe: Mayu 2022 (3%) da Oktoba (2%) a Odisha
  • Tsadar kayayyaki: Kashi 5.9 cikin 100 a Nuwamba 2022.

"Na ga cewa farashin kayan lambu da dangin su wake, ya karu matuka a kasuwa a watanni shida da suka gabata, sai dai a yanzu muna da aiki, har yanzu muna iya saya, “ take fada a daidai lokacin da yaranta biyu suke wasa a can baya.

Farbani ta kuma ce ta daina cin bashi a karamin bankin ba da rance domin sai wa kakanta magani.

"Da yake albashin na karuwa, har mun ma iya biyan wadannan basussukan," kamar yadda take fadi.

Alkaluman tsadar kayayyaki daga Tradingeconomics.com