Chelsea na fargabar rasa Osimhen, Manyan Premier na rububin Cubarsi

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea na fargabar cewa za ta kasa samun sayen dan gaban Napoli Victor Osimhen a bazara, ganin yadda Paris St-Germain da Arsenal suka dage a kan tauraron dan wasan na Najeriya. (Teamtalk)

Ba a sa ran Marcus Rashford ya tafi PSG a bazaran nan mai zuwa, kamar yadda rahotanni ke cewa dan wasan na Ingila da Manchester United zai maye gurbin Kylian Mbappe. (Sky Sports)

Getafe ba za ta iya ci gaba da rike Mason Greenwood fiye da wa'adin zamansa na aro ba, saboda Manchester United za ta sayar da shi ga duk kungiyar da ta saye shi da daraja, inda farashinsa zai kama daga kusan yuro miliyan 50. (Marca)

Manchester City ta yanke shawarar dage tattaunawa a kan sabon kwantiragin dan wasanta na tsakiya Kevin de Bruyne, na Belgium mai shekara 32, wanda kwantiraginsa ya rage saura sama da shekara daya kawai a yanzu. (Football Insider)

Aston Villa na da kwarin gwiwar ci gaba da rike dan wasanta na tsakiya Douglas Luiz, dan Brazil duk da sha'awarsa da Arsenak ke yi. (90min)

Kociyan tawagar Ingila Gareth Southgate ya bayyana cewa ya gaya wa hukumar kwallon kafa ta kasar cewa ta dakatar da maganar makomarsa har sai bayan gasar cin kofin kasashen Turai ta bana, Euro 2024. (Mirror)

Tsohon kociyan Manchester City kuma na Saudiyya a yanzu Roberto Mancini ya zama na farko a matsayin wanda zai maye gurbin Eddie Howe na Newcastle United, idan har kungiyar za ta sauya kociyan nata a bazaran nan. (HITC)

Newcastle na son gaggauta tafiyar Dan Ashworth Manchester United yayin da darektan wasanni na Monaco Paul Mitchell ya kasance na daya a jerin wadanda za su maye gurbinsa. (Telegraph)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Chelsea na son sayen matashin dan bayan Lille Leny Yoro, dan Faransa mai shekara 18 a shawarar da kungiyar ke yi ta neman wanda zai maye gurbin Thiago Silva, mai shekara 39. (Standard)

Manchester United, da Chelsea da kuma Arsenal dukkanninsu suna sha'awar matashin dan wasan Barcelona da Sifaniya Pau Cubarsi, mai shekara 17. (Football Espana)

Fatan Newcastle United da Arsenal na sayen dan bayan Sporting Lisbon, Ousmane Diomande na Ivory Coast, ya karfafa, kasancewar a yanzu Chelsea, wadda ke kan gaba a zawarcinsa sai ta sayar da'yan wasa kafin ta sayi wasu a bazaran nan. (Football Insider)

Manchester City na shirin sayen matashin dan wasan Cardiff City Timeo Whisker, haifaffen Faransa, mai shekara 15, a kan kusan fam 250,000. (Athletic)

Santos ta yi amanna cewa ba makawa Neymar zai sake komawa kungiyar wadda ita ce ta farko da ya yi kafin ya yi ritaya daga wasa. (Mundo Deportivo)

PSV Eindhoven na fatan sayen dan baya Sergino Dest, mai shekara 23, da dan wasan tsakiya Malik Tillman, mai shekara 21, dindindin a bazaran nan ganin yadda 'yan wasan biyu na Amurka suka taka rawar gani a zaman aro a kungiyar daga Barcelona da Bayern Munich. (ESPN)

Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya ta gaya wa takwararta ta Ingila, cewa tana son daukar dan gaban Leeds United Mateo Joseph, haifaffen Sifaniya, wanda ke tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 20, domin sanya shi a tawagar Sifaniya ta 'yan kasa da shekara 21 a wasannin da ke tafe. (AS )

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA za ta ci gaba da kokarin daina maimaita wasanni daga zagaye na uku a kaka mai zuwa. (Mail)