Almeria ta kawo karshen Barca bayan wasa 13 a jere ba a doke ta ba

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gidan Almeria, an kawo karshen wasa 13 da ta yi a jere ba tare da an doke ta ba a La Liga ta bana.
Tun a minti na 24 da fara tamaula Almeria ta ci kwallon ta hannun El Bilal Toure a fafatawar da suka yi a filin wasa Power Horse ranar Lahadi.
Da wannan sakamakon Barcelona ta barar da damar bai wa Real Marid tazarar maki 10 tsakani a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a teburin La Liga da maki 59, ita kuwa Real Madrid ta biyu tana da maki 52.
Almeria, wadda kafin ta karbi bakuncin Barcelona tana tana ta 19 a kasan teburi, yanzu ta yi sama zuwa mataki na 15 da maki 25.
Karo na biyu a jere da aka ci Barcelona a bana, bayan da ta yi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Manchester United a Old Trafford ranar Alhamis.
United ta kai zagayen gaba a gasar Europa League zangon 'yan 16, bayan da ta ci Barcelona 4-3 gida da waje.
Rabon da a doke Barcelona a La Liga tun ranar 16 ga watan Oktoban 2022, inda Real Madrid ta ci 3-1 a Santiago Bernabeu.
Sai dai a cikin Janairun 2023, Barca ta ci Real 3-1 ta lashe Spanish Super Super Cup a Saudi Arabia.
Barcelona wadda ta yi wasa 23 ta ci karawa 19 da canajaras biyu aka doke ta karo biyu a La Liga.
Haka kuma kwallo takwas ne ya shiga ragar kungiyar a kakar nan, wadda ta ci 45 kawo yanzu.
Robert Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a La Ligar kakar nan mai 15.











