Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Carabao Cup: Man City za ta karbi bakuncin Chelsea
Manchester City za ta karbi bakuncin Chelsea a wasan zagaye na uku a Carabao Cup da za su kara ranar Laraba a Etihad.
Manchester City tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal mai jan ragama.
Chelsea kuwa tana bakawi a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana da maki 21.
Wasan da suka buga a tsakaninsu a bara:
2021/2022
Premier League Asabar 15 ga watan Janairun 2022
- Man City 1 - 0 Chelsea
Premier League Asabar 25 Satumba 2021
- Chelsea 0 - 1 Man City
City ta lashe Carabao Cup karo takwas a tarihi, ita kuwa Chelsea tana da biyar, Liverpool ce mai rike da kofin mai tara jumulla, ita ce kan gaba a yawan dauka.
A bara Liverpool ta doke Chelsea a wasan karshe ta dauki Carabao Cup kuma na tara jumulla.
Wasannin da za a buga ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba
- Arsenal da Brighton & Hove Albion
- Newcastle United da Crystal Palace
- Southampton da Sheffield Wednesday
- West Ham United da Blackburn Rovers
- Nottingham Forest da Tottenham
- Wolverhampton da Leeds United
- Liverpool da Derby County
- Manchester City da Chelsea
Wasu batutuwan da ya kamata ku sani kan wasan:
Manchester City
Kalvin Phillips zai koma buga wa Manchester City tamaula a karawar Carabao zagaye na uku da Chelsea ranar Laraba.
Dan wasan ya yi jinyar raunin allon kafada tun cikin watan Satumba, Pep Guardiola ya tabbatar cewar dan kwallon zai yi zaman benci a Etihad.
Joao Cancelo ba zai buga karawar ba, wanda aka yi wa jan kati a wasan Premier League da Fulham, karawar da City ta yi nasara da ci 2-1 ranar Asabar.
To sai dai har yanzu Kyle Walker na jinya.
Chelsea
Kungiyar Stamford Bridge za ta buga wasan ba tare da mai tsaron baya Reece James da Ben Chilwell da kuma Carney Chukwuemeka ba.
Edouard Mendy ne zai tsare raga, bayan da Kepa Arrizabalaga ke jinya, sakamakon aiki da likitoci suka yi masa.