Real Madrid za ta buga wasa tara a cikin watan Afirilu

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta buga wasa tara a cikin watan Afirilu da suka hada a gasar Champions League da La Liga da kuma Copa del Rey.
Real za ta yi wasa shida a La Liga da Champions League fafatawar quarter finals da Chelsea da karawa ta biyu a daf da karshe a Copa del Rey da Barcelona.
Cikin fafatawa taran da za ta yi a cikin watan Afirilu, guda biyar a Santiago Bernabeu za ta yi, sannan ta yi hudu a waje.
Real za ta fara wasa a gida ranar Lahadi 2 ga watan Afirili da Valladolid, kwana uku tsakani ta ziyarci Barcelona domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Copa del Rey.
Ranar 2 ga watan Maris Barcelona ta ci Real Madrid 1-0 a wasan farko a daf da karshe a Copa del Rey a Bernabeu.
Cikin wasa biyar da kungiyoyin biyu za su buga a wasan hamayya da ake kira El Clasico a kakar nan, Barcelona ta yi nasara a uku, Real Madrid ta ci daya.
Wasannin da aka kara tsakanin Real da Barcelona a bana:
Sifanish La Liga Lahadi 19 ga watan Maris 2023
- Barcelona 2 - 1 Real Madrid
Copa del Rey Alhamis 2 ga watan Maris
- Real Madrid 0 - 1 Barcelona
Spanish Super Cup Lahadi 15 ga watan Janairun 2023
- Real Madrid 1 - 3 Barcelona
Sifanish La Liga Lahadi 16 ga watan Oktoban 2022
- Real Madrid 3 - 1 Barcelona
Ranar 8 ga watan Afirilu Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal a karawar La Liga a Santiago Bernabue.
Daga nan ta karbi bakuncin Chelsea a wasan farko a quarter finals a Champions League a Bernabeu ranar Laraba 12 ga watan Afirilu.
Za a buga wasannin mako na 29 a La Liga a karshen mako tsakanin 15 da 16 ga watan Afirilu, inda Real za ta ziyarci Cadiz.
Ranar Talata 18 ga watan Afirilu, Real Madrid za ta je Stamford Bridge, domin buga wasa na biyu a quarter finals da Chelsea a Champions League.
Sauran wasa uku da za ta buga a karshe-karshen watan Afirilu a La Liga za ta yi da Celta Vigo a gida, sannan ta je Girona ta karkare da Almeria a Bernabeu.
Jadawalin wasannin da Real Madrid za ta buga a watan Afirilu.
- Ranar 2 ga watan Afirilu: Real Madrid da Valladolid
- Ranar 5 ga watan Afirilu: Barcelona da Real Madrid
- Ranar 8 ga watan Afirilu: Real Madrid da Villarreal
- Ranar 12 ga watan Afirilu: Real Madrid da Chelsea
- Ranar 15/16 ga watan Afirilu: Cadiz da Real Madrid.
- Ranar 18 ga watan Afirilu: Chelsea da Real Madrid
- Ranar 22/23 ga watan Afirilu: Real Madrid da Celta.
- Ranar 25/26/27 ga watan Afirilu: Girona da Real Madrid.
- Ranar 29/30 ga watan Afirilu: Real Madrid da Almería.









