Ko Real Madrid za ta ci Atletico Madrid a wasan hamayya?

Real Madrid

Asalin hoton, SNS

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Atletico Madrid domin buga wasan mako na shida a gasar La Liga ranar Lahadi.

Real mai maki 15 a mataki na biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya na bukatar cin wasan nan, domin ta sake dare kan teburin.

Ranar Asabar Barcelona ta doke Elche da ci 3-0 a Camp Nou, Lewandowski ne ya ci biyu daga ciki a fafatawar.

Hakan ya sa kungiyar ta Camp Nou ta hau kan teburin La Liga da maki 16, bayan buga karawa shida a gasar bana.

Atletico ta ci wasa tara daga 14 baya da ta yi a gida da Real da canjaras biyu da shan kashi a guda uku.

Morata ya ci kwallo uku a kakar La Liga ta bana, shi ne kan gaba a kungiyar a cin kwallaye a gasar.

A Real kuwa Karim Benzema ne na farko mai biyar a raga, wanda ba zai buga wasan Lahadi ba, bayan da yake jinya.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Koci, Diego Simeone zai ja ragamar wasan hamayya 22 tsakanin kungiyoyin biyu a La Liga, zai yi kan-kan-kan da Luis Aragonés, wajen yawan fuskantar Real a wasannin hamayya a kungiyar.

Shi kuwa kociyan Real, Carlo Ancelotti ya yi rashin nasara a wasa hudu daga shida da ya fuskanci Simeone.

Wasan da suka buga a bara

2021/2022

La Liga Lahadi 8 ga watan mayun 2022   

  • Atl Madrid       1 - 0     Real Madrid   

La Liga Lahadi 12 ga watan Disambar 2022             

  • Real Madrid    2 - 0     Atl Madrid      

Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan kwallon da ya je da su gidan Atletico Madrid, domin buga wasan na hamayya.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos.

Masu cin kwallaye Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.