Carroll ya koma Bordeaux bayan barin Amiens

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila da Liverpool, Andy Carroll ya koma Bordeaux mai buga gasa mai daraja ta huɗu a Faransa, bayan da ya bar Amiens.
Carroll, mai shekara 35, zai koma taka leda a gasa mai daraja ta huɗu a Faransa, duk da karawa huɗu da ya yiwa Amiens mai buga Ligue 2 a kakar nan.
Ya ci ƙwallo huɗu a wasa 35, tun bayan da ya koma Faransa da taka leda a Satumbar 2023 daga Reading, bayan da ƙwantiraginsa ya kare.
Bordeaux mai kofin Ligue 1 guda shida ta bar buga gasar ƙwararru a watan Yuli, bayan barin Ligue 2 zuwa Championnat National 2, sakamakon talaucewa da ta yi.
Lokacin da Carroll ya buga Premier League ya ci ƙwallo 54 a wasa 248, wanda ya taka leda a Newcastle da Liverpool da kuma West Ham.
Carroll ya ci wa Ingila ƙwallo biyu a wasa tara da ya buga mata, daga cikin tawagar da ya zura wa ƙwallo har da Sweden a Euro 2012.
Ana sa ran Carroll zai fara yiwa Bordeaux tamaula ranar Asabar a wasan da za ta kara da Voltigeurs de Chateaubriant.






