Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alexander-Arnold ba zai buga wa Ingila karawa da Jamus ba
Dan wasan Liverpool, Trent Alexander-Arnold baya cikin 'yan wasan tawagar Ingila da za su kara da Jamus a Nations League ranar Litinin a Wembley.
Alexander-Arnold, wanda jinya ta hana shi buga wasan karshe a Euro 2020, ya yi wa Ingila karawa daya a shekarar nan, ya kuma yi zaman benci a ranar Juma'a da Italiya ta ci 1-0.
Sauran da ba sa cikin wadanda za su buga wasan na hamayya sun hada da Fikayo Tomori da Jarrod Bowen da kuma James Ward-Prowse.
To sai dai dan kwallon Brentford, Ivan Toney yana daf da fara buga wa Ingila wasan farko.
Wannan shi ne karon farko da tawagar Ingila ta gayyaci Toney, wanda ya ci kwallo biyar a gasar Premier ta bana, amma ba a saka shi a karawa da Italiya ba.
Yana cikin 'yan kwallo Ingila 23 da aka bayyana don fuskantar Jamus a wasan ranar Litinin, sai dai dan wasan Manchester City, Jack Grealish yana hutun hukuncin dakatarwa.
Tuni Ingila ta bar gasar Nattions League mai daraja ta daya, bayan da ta yi ta karshe a rukunin da take ciki a wasa biyar da ta kara a kakar nan.