Sabon ɗan wasan Arsenal Merino ya ji rauni a atasayensa na farko

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce sabon ɗan wasan da suka saya Mikel Merino zai yi jinyar makonni bayan raunin da ya ji a kafaɗrsa yayin atasayensa na farko a ƙungiyar.

Ɗan Sifaniyan ya koma Arsenal ne kan fan miliyan 31.6 daga Real Socieded ranar Talata.

Merino ne na biyu da Arsenal ta ɗauka a bana bayan Riccardo Calafiori daga Bologna, kuma a ranar Alhamis ya fara atasayen.

Ɗan wasan mai shekara 28 ya yi karo ne da wani abokin wasansa, abin da ya jawo "ƙaramar tsagewa" da za ta saka shi jinya "ta 'yan makonni".

"Eh abin takaici. Jiya ya gamu da hatsari har ma ya ji ciwo a kafaɗa. Da alama zai yi makonni yana jinya," in ji Arteta.

"Yana cike da karsashi sosai, kuma abubuwa na tafiya yadda ya kamata. Ya faɗi ne a ƙasa sai kuma Gabi ya faɗo a kansa. Za mu jira dai mu gani amma abin bai yi tsanani ba, za mu yi gwaje-gwaje."

Arsenal ta ci duka wasanninta biyu na farko a gasar Premier League da ta buga da Wolves da kuma Aston Villa.

A ranar Asabar kuma za ta karɓi baƙuncin Brighton, wadda ta cinye nata wasannin ita ma.