Ƙasashen Afirka da suka daina amfani da maganin Benylin na Johnson&Johnson

    • Marubuci, Makuochi Okafor & Aaron Akinyemi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3
Benylin Paediatric cough syrup has been recalled in at least five African countries

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Benylin Paediatric cough syrup has been recalled in at least five African countries

Aƙalla ƙasashen Afirka biyar sun yi kira da a daina amfani da maganin tari na Johnson & Johnson bayan gwaje-gwaje sun nuna maganin tarin na da sinadarin diethylene glycol mai guba kuma mai iya yin kisa.

Hukumar kula da magunguna ta Kenya ta sanar a makon da ya gabata cewa ta hana amfani da wani rukunin maganin tari na Benylin Pediatric.

Wannan ya biyo bayan sanarwar makamanciyar wannan daga hukumar kula da magunguna ta Najeriya (Nafdac).

Ita ma Afirka ta Kudu ta ce ta hana amfani da nau'ikan magugunan tari guda biyu yayin da kuma Rwanda da Tanzaniya suka haramta amfani da wani maganin tari guda ɗaya.

Hukumar Kula da Magunguna da Guba ta Kenya (PPB) ta ce kamfanin Johnson & Johnson ne suka yi maganin tarin da aka haramta amfani da shi a Afirka ta Kudu a watan Mayun 2021, tare da ranar da zai lalace a watan Afrilu 2024. PPB ɗin ta faɗi hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fara bincike kan lamarin.

Har ila yau, hukumar ta shaida wa BBC cewa tana bayar da sanarwar faɗakar da jama'a a duk faɗin kasar tare da shawartar mutane da su mayar da magungunan tarin ga wadanda ke kawo musu.

Hukumar ta kuma umarci cibiyoyin kiwon lafiya da su keɓe magungunan tarin nan take tare da dakatar da rarrabawa da kuma sayar da shi.

Karim Wanga, shugaban hukumar da ke sa-ido kan tallace-tallace na PPB, ya ce hukumar ta umurci wakilin gida da ke da alhakin shigo da samfurin maganin tarin a Kenya ya keɓe sauran maganin da aka shigo da su kwanan nan don gwaji, gami da waɗanda faɗakarwar ba ta shafa kai tsaye ba, don tantance girman gurbacewarsu.

A halin yanzu ana gudanar da bincike a dakin gwaje-gwaje, kuma hukumar na jiran sakamakon don yanke hukunci idan wani mataki ya zama dole.

Kenvue, wanda yanzu ya mallaki kamfanin Benylin bayan ya rabu da kamfanin Johnson & Johnson a bara, ya shaida wa BBC cewa "lafiya da aminci" na mutanen da ke amfani da kayayyakinsu su ne "mafi fifiko" kuma suna ɗaukar lamarin "da mahimmanci" .

Kamfanin ya kuma bayyana a cikin wata sanarwa cewa yana aiki tare da hukumar kula da magunguna ta Najeriya, Nafdac, wajen gudanar da tantancewar da suka hada da "tabbatar da sahihancin samfurin maganin tarin da tsarin gwajin da aka yi amfani da shi da kuma sakamakon da hukumar ta bayar".

Ana ci gaba da gudanar da bincike bayan da aka gano maganin tari na yara na Benylin yana da yawan sinadarin diethylene glycol mai guba.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Ana ci gaba da gudanar da bincike bayan da aka gano maganin tari na yara na Benylin yana da yawan sinadarin diethylene glycol mai guba.

Me ya sa rukunin maganin tarin da aka haramta ke da haɗari sosai?

A cewar hukumar Nafdac, sinadarin diethylene glycol na iya haifar da matsalolin lafiya masu tsanani, waɗanda suka haɗa da ciwon ciki da amai da gudawa, da kuma mummunan rauni na koda.

Tun daga shekarar 2022 ne Diethylene glycol ke da alaƙa da mutuwar yara da dama a ƙasashen Gambia da Uzbekistan da Kamaru a daya daga cikin mummunar guba mafi muni a duniya.

Bayan da aka bayar da rahoton mutuwar mutane a Kamaru da Gambia, an ba da sanarwar duniya game da maganin tari guda huɗu da kamfanin Indiya mai suna Maiden Pharmaceuticals ya yi.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta danganta maganin da mutuwar yara 66 kuma ta ce ta gano tsananin gubar da ke cikin magungunan.

"Muna da shaidu, mun gwada waɗannan magungunan," in ji Amadou Camara, shugaban kwamitin majalisar dokokin Gambia da ya binciki mutuwar.

"Sun ƙunshi adadin sinadaren ethylene glycol da diethylene glycol da ake shigo da su kai tsaye daga Indiya wanda Maiden ta kera su."

Musanta alaƙar mutuwar yara da maganin tari

Maiden Pharmaceuticals da gwamnatin Indiya sun musanta wata alaka tsakanin maganin tari da mutuwar yara.

A cikin Disamban 2023, Indiya ta bayyana cewa magungunan tarin sun cika ka'idoji masu inganci lokacin da aka gwada su cikin gida.

Kasar ta kuma ba da sanarwar ɗaukar matakan wajabta wa kamfanoni su tabbatar an gwada samfurin maganin tari a dakunan gwaje-gwajen da gwamnati ta amince da su kafin fitar da su.

Tun daga watan Yulin 2023, Gambiya ta kuma aiwatar da wannan buƙatun gwaje-gwaje na magungunan da ake fitarwa daga Indiya.

Indiya ta fitar da magunguna da darajarsu ta kai dala biliyan 25.4 a cikin shekarar da ta ƙare na 2023 a watan Maris.

Daga cikin wannan, an fitar da dala biliyan 3.6 zuwa ƙasashen Afirka.