Hernandez na Faransa ya gama buga Gasar Kofin Duniya a Qatar

An wallafa

Mai tsaron bayan Faransa, Lukas Hernandez ya gama buga Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, bayan da ya ji rauni a wasa da Australia ranar Talata.

Mai shekara 26, mai taka leda a Bayern Munich ya ji rauni a lokacin da ya fadi da gwiwar kafa daf da Australia za ta ci kwallo a wasan da aka doke ta 4-1.

An tabbatar da girman raunin da Hernandez ya ji ranar Laraba, bayan da aka yi masa gwaje-gwaje.

An canji Hernandez da dan uwansa Theo, wanda ke taka leda a AC Milan, daga nan Faransa ta farke ta kara kwallo uku a karawar rukuni na hudu.

Wadanda suka ci wa mai rike da kofin duniya kwallayen sun hada da Adrien Rabiot da Kylian Mbappe da Olivier Giroud wanda ya zuba biyu a raga.

'Yan wasan Faransa da dama na jinya daf da za a fara Gasar Cin Kofin Duniya, ciki har da dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema.

Bayan da aka sanar da raunin Benzema, Faransa bata maye gurbin dan wasan mai shekara 34 ba, hakan ya sa ta je da 'yan kwallo 25 a Qatar, yanzu saura 24.

Tun farko Paul Pogba da N'Golo Kante ba sa cikin koshin lafiya da ya kamata Faransa ta gayyace su babbar Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.

Haka shima mai tsaron baya, Presnel Kimpembe ya hakura da wasannin, wanda aka maye gurbinsa da Axel Disasi.

Shi kuwa mai taka leda a RB Leipzig, Christopher Nkunku ya ji rauni a lokacin atisaye a tawagar Faransa, inda aka maye gurbinsa da Randal Kolo Muani.