Arsenal na tangal-tangal a kokarin lashe Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta tashi 2-2 a gidan West Ham United a wasan mako na 31 a gasar Premier League ranar Lahadi.
Hakan ya sa Arsenal wadda ke jan ragamar teburin Premier na sassarfa a shirin da take na lashe Premier a karon farko bayan 2003/04.
Gunners ce ta fara cin kwallo biyu, kan hutu West Ham ta zare daya, sannan ta farke na biyu a wasan na hamayya na kungiyoyin birnin Landan.
Gabriel Jesus da Martin Odegaard ne suka ci wa Arsenal kwallayen a minti 10 da take leda a karawar da suka yi a London Stadium.
Kamar yadda Arsenal ta barar da maki a Liverpool, wadda ta fara cin biyu daga baya aka farke a Anfield, haka ta kara sakaci a fafatawa da West Ham United.
Said Benrahma ne ya ci wa West Ham na farko a bugun fenariti, baya da Gabriel ya yi wa Lucas Paqueta keta a cikin da'ira ta 18.
Arsenal ma ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da Michail Antonio ya taba kwallo da hannu, amma Bukayo Saka ya barar.
West Ham ta farke na biyu kasa da saura minti uku lokaci ya cika ta hannun Jarrod Bowen, bayan da ya samu kwallo daga wajen Thilo Kehrer.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Minti biyar aka kara inda Arsenal ta yi kokarin kara na uku amma hakan bai samu ba, Antonio ya kusan kara ci wa West Ham na uku a karawar.
Arsenal ta doke West Ham 3-1 ranar 26 ga watan Disamba a wasan farko a Premier ta bana a Emirates.
West Ham tana nan a matakinta na 15 a kasan teburi, amma da tazarar maki hudu tsakaninta da 'yan ukun karshe a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Arsenal ta je West Ham a matakin farko a teburi da tazarar maki shida tsakaninta da Manchester City ta biyu, yanzu ya koma saura hudu.
Ranar Asabar Manchester City wadda take da kwantan wasa ta casa Leicester City 3-1 a Etihad a wasan mako na 31 a Premier League.
Saura wasa bakwai ya rage wa Gunners, wadda za ta karbi bakuncin Southampton ranar Juma'a daga nan ta je gidan Manchester City ranar 26 ga watan Afirilu.
Jerin wasannin da suka rage wa Arsenal:
Premier League Juma'a 21 ga watan Afirilu
- Arsenal da Southampton
Premier League Laraba 26 ga watan Afirilu
- Man City da Arsenal
Premier League ranar Talata 2 ga watan Mayu
- Arsenal da Chelsea
Premier League Lahadi 7 ga watan Mayu
- Newcastle da Arsenal
Premier League Lahadi 14 ga watan Mayu
- Arsenal da Brighton
Premier League Asabar 20 ga watan Mayu
- Nottm Forest da Arsenal
Premier League Lahadi 28 ga watan Mayu
- Arsenal da Wolves











