Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An jefa bam ɗin fetur a wani sansanin MDD da ke Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo
An jefa bam ɗin fetur a wani sananin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Beni a Gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar ƙin jinin majalisar dinkin duniya a ƙasar.
Wani mai magana da yawun majalisar ya ce masu zanga-zangar sun hari aƙalla sansanoni biyu na majalisar a ranar Alhamis.
Ya bayyyana cewa ƴan tawaye ɗauke da makamai daga ƙungiyar Mai-Mai sun shiga zanga-zangar a arewacin Kivu, yankin da dandazon jama'a suka yi ta fitowa zanga-zanga.
Aƙalla mutum 19 aka kashe ciki har da jami'an wanzanar da zaman lafiya na majalisar sakamakon wannan zanga-zanga.
Yanayin da ake ciki a Gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo na ƙara ƙazanta, kusan mako guda kenan bayan an soma zanga-zangar ƙin jinin Majalisar Dinkin Duniya.
Da yammacin jiya Alhamis, masu zanga-zangar sun jefa bam ɗin fetur a sansanonin majalisar da ke a Boikene da Beni.
Babu tabbaci kan waɗanda suka rasu ko kuma suka jikkata.
Wani mai magana da yawun majalisar ya shaida cewa mayaƙan ƙungiyar Mai-Mai sun shiga cikin masu zanga-zangar a Butembo, wanda hakan ake kallo a matsayin abin da ya ƙara rura wutar wannan rikici. An soma wannan zanga-zanga ne a ranar Litinin inda mutane suka rinƙa zargin jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen kare farar hula daga harin ƴan tawaye da sauran ƙungiyoyi masu riƙe da makamai.
Shirin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Congo na da zaratan sojoji dubu sha takwas, wanda shiri ne na biyu mafi girma a duniya, sai dai yana shan suka a wani lokacin sakamakon gazawa wajen kawo zaman lafiya a ƙasar. Sama da ƙungiyoyi 100 daban-daban na masu riƙe da makamai ke kai hare-hare a ƙasar, ciki har da ƙungiyar Allied Democratic Front wadda ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.
An kashe ɗaruruwan mutane, dubbai kuma sun rasa muhallansu sakamakon hare-haren baya-baya da ƙungiyoyin suka dawo kaiwa.