Mount ya ci Aston Villa kwallo biyu da Chelsea ta koma ta hudu

An wallafa

Chelsea ta doke Aston Villa da ci 2-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka kara ranar Lahadi a Villa Park.

Minti shida da fara wasa, Chelsea ta zura kwallo a raga ta hannun Mason Mount, shi ne ya kara na biyu a zagaye na biyu a karawar.

Wannan shi ne karo na uku da Mount ya ci kwallo biyu ko fiye da haka a Premier League da yake yi wa Chelsea.

A kakar 2021 cikin watan Oktoban, Mason ya ci Norwich City uku, sannan ya zura biyu a ragar Southampton cikin watan Aprilun 2022.

Sabon koci, Graham Potter ya ci wasa uku a jere da fara jan ragamr Chelsea a Premier League a kakar nan, tun bayan da ya maye gurbin Thomas Tuchel.

Da wannan sakamakon Chelsea wadda ta yi wasa takwas a babbar gasar tamaula ta Ingila, tana ta hudu a teburin Premier da maki 16.

Ranar 19 ga watan Oktoba, Chelsea za ta ziyarci Brentford a wasanta na gaba a Premier League.

Ita kuwa Aston Villa za ta ziyarci Fulham ranar Alhamis 20 ga watan Oktoba.