Brazil ta ci gaba da zama ta daya a tamaula a duniya

Brazil Male national team

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tawagar Brazil ta ci gaba da zama ta daya a fagen tamaula a duniya, bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fitar da jadawalin kasashen ranar Alhamis.

Bayan da Brazil ke mataki na daya, Belgium ce ke biye da ita, sai Argentina ta uku, wadda ta maye gurbin Faransa mai rike da kofin duniya.

Faransa ta koma ta hudu wadda ta ci karo da koma baya, sakamakon kasa cin wasa a karawa hudu a Nations League. 

Ingila ta ci gaba da zama a mataki na biyar, sai Sifaniya da ta koma ta shida ta hau kan Italiya, wadda ke rike da Euro 2020, wadda ta koma ta bakwai.

Tawagar Netherlands ce ta takwas, sannan Portugal ta tara da kuma Denmark, wadda take cikin goman farko.

Mexico ta fita daga jerin goman farko, wadda take ta tara a baya, yanzu ta koma ta 12 tana biye da Jamus ta 11.

Fifa Ranking

Asalin hoton, Fifa

Jerin goman farko a tamaula a Afirka

  • Senegal
  • Morocco
  • Tunisia
  • Nigeria
  • Kamaru
  • Masar
  • Algeria
  • Mali
  • Cote d'Ivoire
  • Burkina Faso