Ko Chelsea za ta hada maki uku a kan Newcastle United?

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea za ta karbi bakuncin Newcastle United a wasan mako na 28 a gasar Premier League da za su kara ranar Litinin a Stamford Bridge.
Chelsea mai maki 36 tana ta 11 a teburin Premier League, ita kuwa Newcastle mai maki 40 tana ta 10.
Wasa biyu suka kara a bana kakar 2023/2024
League Cup Talata 19 ga watan Disambar 2023
- Chelsea 1 - 1 Newcastle
Premier League Asabar 25 ga watan Nuwambar 2023
- Newcastle 4 - 1 Chelsea
Labarin da ya shafi kungiyoyin:
Chelsea za ta buga karawar ba tare da mai tsaron baya, Ben Chilwell da Levi Colwill ba, wadanda ke jinya.
Conor Gallagher bai da lafiya, sai dai har yanzu Carney Chukwuemeka da Reece James da Benoit Badiashile da Christopher Nkunku duk suna jinya.
Newcastle za ta kara a wasan ba tare da Kieran Trippier ba wanda ke jinya.
Lewis Hall ba zai fuskanci kungiyarsa ba, yayin da har yanzu Callum Wilson da Joelinton da Nick Pope sun dade suna jinya.
Abinda ya kamata ku sani kan wasa:
Wasa daya Chelsea ta yi rashin nasara daga 28 baya da ta kara da Newcastle a Premier League, wadda ta ci 20 da canjaras bakwai.
Chelsea na fatan yin nasara biyu a jere a kan Newcastle a karon farko tun bayan 1986-87.
Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Wasa daya Chelsea ta rasa daga 12 da ta yi a gida a dukkan fafatawa da cin takwas da canjaras uku.
Chelsea ba ta yi rashin nasara ba a Premier League a gida a cikin watan Maris tun daga 2001, kenan karawa 37.
Saura maki daya Chelsea ta yi kan-kan-kan da yawan wanda ta hada a gabaki dayan kakar bara.
Cole Palmer yana da hannu a cin kwallo 17 daga karawa 18 a Chelsea, wanda ya ci 10 ya bayar da bakwai aka zura a raga.
Palmer shi ne kan gaba a yawan cin kwallo da bayarwa a zura a raga tsakanin 'yan Chelsea masu shekara 21.
Newcastle United

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta yi rashin nasara shida daga karawa takwas a Premier League da cin biyu daga ciki.
An zura kwallo 29 a ragar Newcastle a wasannin waje a lik, Sheffield ce wadda aka fi zura mata kwallaye a waje fiye da ta kungiyar St James Park.
Eddie Howe ya yi nasara hudu daga wasa bakwai da ya fuskanci Chelsea a matakin koci da canjaras biyu da rashin nasara daya.
Anthony Gordon ya ci kwallo 10 ya bayar da biyar aka zura a raga a wasa 27 a Premier League a bana.











