Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ingila ta gayyaci Jordan Hendersen na Liverpool
An gayyaci kyftin din Liverpool, Jordan Henderson cikin tawagar Ingila da za ta buga wasa da Italiya da Jamus a Nations League. .
Tun farko ba a bayyana Hendersen, mai shekara 32 cikin jerin 'yan wasan da Gareth Southgate ya sanar ba ranar Alhamis, sakamakon jinya da yake yi.
Sai dai mai buga tamaula daga tsakiya ya murmure, dalilin da ya sa aka mika masa goron gayyatar, wanda tuni yana sansanin horon 'yan wasan Ingila a St George Park.
Hendersen ya maye gurbin dan wasan Manchester City, Kalvin Phillips, wanda ke jinyar raunin allon kafata da ya ji a wasan sada zumunta da Barcelona.
Dan kwallon Liverpool ya buga wa Ingila wasa 69, bai yi wa kungiyar Anfield karawa uku baya ba, sakamakon raunin da ya ji a wasa da Newcastle United ranar 31 ga watan Agusta.
Liverpool ta doke Newcastle 2-1 a wasan Premier League da suka fafata a Anfiled, inda aka fara cin Liverpool a wasan daga baya ta farke ta kara na biyu daf da za a tashi wasan.
Sai dai wasa daya kwal Hendersen ya yi wa Ingila a 2022, shi ne na sada zumunta da ta doke Switzerland 2-1 a Wembley a cikin watan Maris.
Ingila za ta fafata da Italiya a San Siro ranar Juma'a, sannan ta karbi bakuncin Jamus a Wembley ranar Litinin.