Chelsea ta amince ta dauki Aubameyang daga Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta amince da cinikin dan wasan gaban Barcelona Pierre-Emerick Aubameyang da yakai fan miliyan 12, hadi da Marcus Alonso, kamar yadda Guillem Balague ya bayyana.
Aubameyang ya ci kwallo 13 a wasa 24 da ya bugawa Barcelona bayan komawa kungiyar Spaniyan daga Arsenal a watan Janairu.
Duk kungiyar da za ta dauki dan wasan kafin karewar kwantaraginsa sai ta biya yuro miliyan 100 kan dan wasan da ya buga minti takwas kacal a wannan kakar.
Dan wasan mai shekara 33 zai zama na bakwai da Chelsea ta saya a wannan kakar.
Kungiyar ta sayi dan wasan bayan Faransa Wesley Fofana kan kudin da yakai fan miliyan 70, Raheem Sterling daga Manchester City kan fan miliyan 50, sai dan bayan Senegal Kalidou Koulibaly daga Napoli kan fan miliyan 34, akwai Carney Chukwuemeka daga Aston Villa kan £20m.
Sauran sun hada dan wasan bayan Spaniya Marc Cucurella daga Brighton kan £60m sai kuma dan kasar Italiya Cesare Casadei daga Inter Milan.
Da wannan cinikin na Aubameyang mai kungiyar ta Chelsea Todd Boehly ya kashe kimanin fan miliyan 250 kenan a shekararsa ta farko bayan maye gurbin Roman Abramovich.











