Halin da aka shiga a Rasha bayan haɗarin jirgin shugaban Wagner

An wallafa

Al'ummar Rasha sun cika da mamaki.

Mutane sun kaɗu sanadiyyar hare-haren jirage marasa matuƙa a tsakiyar birnin Moscow waɗanda suka riƙa lalata gine-gine.

Haka nan takardar kuɗin ƙasar ta yi mummunar faduwa - lamarin da ya kai ga dalar Amurka guda ta haura rouble 100.

Sai kuma gazawar da Rasha ta yi na tura kumbo zuwa wata, inda ya yi ɓatar-dabo a sararin samaniya.

Sai kuma ga labarin hatsarin jirgin shugaban mayaƙan Wagner, Yevgeny Prigozhin a ranar Laraba.

Duk da cewa labari ne mai nauyi amma bai zo da mamaki ba, domin wasu Rashawan sun yi tunanin cewa hakan zai iya faruwa tun tuni?

An kwashe makonni ana shaci-faɗi a Rasha kan makomar Prigozhin.

Yanzu wata biyu ke nan cif bayan da shugaban na Wagner ya jagoranci wani bore a ƙasar ta Rasha.

Mayaƙansa sun ƙwace wani birni a Rasha sannan suka yi yunƙurin tunkarar babban birnin ƙasar (Moscow).

Bayan wannan bore, mutane da dama na da yaƙinin cewa kwanakin Prigozhin sun kusa ƙarewa.

Ganin cewa boren mummunan cin fuska ne shugaba Putin da fadarsa ta Kremlin.

Sai dai Putin mutum ne wanda ba ya mantuwa kuma ba ya yafiya.

Kimanin sa'a ɗaya bayan hatsarin jirgin, Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Rasha (Rosaviatsiya) ta fitar da sanarwa inda ta tabbatar da cewa sunan Yevgeny Prigozhin na cikin jerin fasinjojin da ke cikin jirgin.

Wannan tamkar wani azarɓaɓi ne da ba a saba gani ba daga hukumar. Kasancewar ba a san ta da hanzari irin haka ba.

Kafar talabijin ta Rasha ba ta mayar da hankali sosai wajen kawo rahoton hatsarin jirgin ba.

A ɓangaren ƙungiyar Wagner kuwa, wani shafin kafar Telegram da ke da alaƙa da ita ya yi iƙirarin cewa 'maƙiya Rasha sun kashe' Prigozhin.

A cibiyar kamfanin na Wagner an kafa wani tanti, kuma kafafen yaɗa labarai na Rasha sun wallafa hotuna da ke nuna yadda mutane ke ajiye furanni na alhini.

Yanzu hankali ya koma kan ko mene ne ya faru da jirgin.

Majiyoyi daga Rasha na cewa ana bincike kan abubuwa da dama, ciki har da ko akwai yiwuwar sanya hannun wasu daga ƙasashen waje.

Lokacin da ta yi tsokaci kan lamarin, wata mai sharhi kan lamurra, Tatiana Stanovaya ta ce abin da ya haddasa hatsarin ba shi ne mafi muhimmanci ba, abu mafi muhimmanci shi ne saƙon da wannan lamari zai isar ga duk wani mai yunƙurin bore:

"Kowa zai kalli wannan lamari a matsayin ramuwa daga ɓangaren Putin, mutuwar Prigozhin za ta zamo darasi."