Harin lashe zinare: Afirka na fatan cin lambobin yabo a gasar duniya

f

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Masu bibiyar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle a fadin Afirka sun karkata akalarsu zuwa Budapest babban birnin kasar Hungary, domin halartar gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya.

A gasar bara a Oregon Habasha da Kenya sun zo na biyu da na hudu a teburin gasar, amma sauran kasashen Afirka ba su taka rawar gani ba.

Jimillar lambobin yabo 28 ne aka raba tsakanin kasashe bakwai kacal, inda Moroko da Najeriya da Uganda suka bi sahun Habasha da kuma Kenya a samun a kalla zinari daya.

To ko shin nahiyar za ta iya inganta wannan yukurin idan aka fara gasar a ranar Asabar 19 ga watan Agusta?

BBC zai dukufa a wani yunkuri na za kulo wadanda za su fafata a gasar.

Fatan yin abin kirki

A cikin dukkan 'yan wasan Afirka da za su fafatawa a Budapest, 'yan kalilan a ke sa ran za su taka rawar gani wadanda za su samu lambar zinari kamar fitacciyar jarumar nan ta Kenya, Faith Kipyegon, wadda mutane da yawa ke kallonta a matsayin wacce ta fi kowacce mace gudun mita 1500 a tarihi.

A cikin gasar duniya ko ta Olympics guda biyar da aka yi tun a shekarar 2016, 'yar shekaru 29 ta rasa zinari sau daya ne kawai - kuma a shekarar 2019 ne inda gasar Doha ta gudana watanni 15 bayan Kipyegon ta haifi 'yarta.

Baya ga kambunta biyu na gasar Olympics da na duniya guda biyu, Kipyegon ta kuma kafa tarihin tseren mita 1500 a watan Yuni. Mako guda bayan haka, ta ba wa mutane da yawa mamaki ta hanyar kafa tarihin tseren mita 5000 - a tseren da ta yi na uku mai wannan nisan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gudaf Tsegay ta kare a bayan Kipyegon a tseren mita 1500 a Oregon a bara. Amma 'yar Habashan za ta mayar da azurfa zuwa zinari bayan kwanaki biyar a lokacin da ta samu kambu mafi girma a rayuwarta a gudun tseren mita 5000.

'Yar wasan mai shekaru 26 ta ce yanzu ta mayar da hankali kan gudu mai nisa, a kwanan baya ta shaida wa BBC cewa, "Ina son sake lashe gasar duniya".

Dan kasarsu Tsegay, Letesenbet Gidey, shi ne zakaran tseren mita 10,000 kuma ko shakka babu zai sake zama dan takara a Budapest.

Mai neman ci gaba da rike kambun da aka ci a Oregon shi ne dan wasan Maroko Soufiane El Bakkali, zakaran Olympic kuma wanda ya ayyana kansa "sarkin tseren steeplechase".

Dan wasan mai shekaru 27 ya taka rawar gani yayin da ya kawo karshen mulkin Kenya na tsawon shekaru 15 a karshe kuma ya nufi Hungary ba tare da an doke shi ba tun watan Satumban 2021.

Dan kasar Habasha Lamecha Girma ya samu damar samun azurfa a dukkan wasannin biyun da El Bakkali ya lashe, amma ya nuna bajintarsa a watan Yuni lokacin da dan wasan mai shekaru 22 ya kafa tarihi a birnin Paris, yayin da ya kammala tseren a lokaci 7:52.11, inda ya yanke kusan dakika biyu cikin karancin lokacin da aka kafa. shekaru 19 a baya.

Dan kasar Kenya Simon Koech, mai shekaru 20, shi ma ya kasance mai tasowa a gasar tseren mita 3,000 nau’in Steeplechase. Ya na da lokaci na uku mafi sauri a duniya a bana bayan Girma da El Bakkali.

Soufiane El Bakkali celebrates winning steeplechase gold at the 2022 World Athletics Championships

Asalin hoton, Getty Images

A tseren mita 10,000 na maza, Joshua Cheptegei na Uganda ne ke neman lashe gasar duniya karo na uku a jere.

Idan ya cimma burinsa, dan wasan mai shekaru 26 zai kusa kwatanta nasarorin da fitaccen dan wasan Habasha Haile Gebrselassie da Kenenisa Bekele suka samu, wadanda dukkansu suka lashe gasannin duniya hudu a jere.

Kalubalen da ke hanyar Cheptegei na samun daukaka ya ragu sosai bayan da dan kasarsa Jacob Kiplimo, mai shekaru 22, ya fice sakamakon raunin mako guda kafin a fara gasar a Budapest, amma ‘yan kasar Habasha.

Berihu Aregawi da Selemon Barega, wadanda suka fi sauri a duniya har zuwa wannan kakar, za su ingiza Cheptegei.

Gudun neman nasara

'Yan wasa suna shafe watanni, idan ba shekaru ba, suna shirye-shiryen yin nasara a manyan gasanni, don haka ba zai yi wuya a fahimci fushin masu fafatawa da ke samun cikas ba, saboda batutuwa a gabnnin gasar ta Oregon.

Dan wasan gudu dan kasar Kenya, Ferdinand Omanyala na cikin wadanda suka sha wahala saboda tsananin bukatun shiga Amurka da kuma rikice-rikicen cutar Korona a inda zakaran tseren mita 100 na Afirka ya karbi bizarsa kwana daya kacal da fara tserensa na farko.

Ya sauka sa'o'i uku kafin tseren share fage na farko, game da kammalawa da jami’an kwastam na shige da fice, bai sami lokacin da zai shirya wa tseren yada ya kamata ba.

Mai shekaru 27 ya kai wasan dab da na karshe, amma zai yi fatan kara yin gaba sosai a Budapest, haka kuma Akani Simbine na Afirka ta Kudu wanda ya zo na biyar a gasar tseren mita 100 a Oregon.

Ferdinand Omanyala of Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Wani wanda za'a kalla shine zakaran duniya na 'yan kasa da shekaru 20 na Botswana, Letsile Tebogo, wanda shi ma ya kai wasan kusa da na karshe na mita 100 a bara, bayan da ya zama mafi karancin shekarun da ya lashe gasar tseren mita 200 na Afrika.

Kamar Tebogo, dan kasar Laberiya Joseph Fahnbulleh zai fi kai hari kan tseren mita 200 a Budapest, bayan da kadan ya kuskure wajen samun lambar yabo a Oregon.

Wayde van Niekerk na iya sa ran cewa za a sa masa ido sosai yayin da mai tseren mita 400 ke ci gaba da dawowar sa mai ban sha'awa bayan shekaru shida da ya yi fama da rauni, inda ba a doke dan Afirka ta Kudun ba a wasanni uku na gasar Diamond League kawo yanzu.

Mai yiwuwa shi ne na hudu mafi sauri a duniya a bana, amma ya ci gaba da zama a bayan zakaran Commonwealth na Zambia, Muzala Samukonga, wanda shi ne na biyu a jerin masu shiga gasar da lokaci dakika 43.91.

Dan wasan mai shekaru 20 yana fama da rauni amma idan aka jingine wadannan matsalolin, masana za su sa ido don ganin ko zai iya sake taka rawar da ya taka a bara inda ya lashe lambar zinari a gasar da aka gudanar a Birmingham.

A cikin tseren mata, Marie-Josee Ta Lou za ta yi fatan cigaba da zafin naman da ta ke da shi.

'Yar Ivory Coast din- wacce ta kafa tarihin tseren mita 100 na Afirka da lokaci 10.78 a shekarar 2021 - ta zo ta bakwai a wasan karshe na bara wanda Shelly-Ann Fraser-Pryce ta Jamaica ta lashe.

Duk da cewa tana da shekaru 34 a yanzu, Ta Lou na iya tunanin cewa Fraser-Pryce tana da shekaru 35 a lokacin da ta ketare layin don lashe kambunta na biyar a duniya.

Zango?

Burkina Faso ta samu nasara a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a karon karshe lokacin da babban dan wasan kasar, Hugues Fabrice Zango, mai tsalle-tsalle, ya karbi azurfa - ci gaba kan tagullan da ya samu a shekarar 2019.

Babu wani dan wasan Burkina Faso da ya taba samun lambar yabo a gasar, kuma tun da ya ci lamba ta farko a gasar Olympics, a gasar Tokyo, Zango a yanzu yana kallon zinari, zuwa yanzu bai sami daman lashewa ba a fagen duniya.

Sai dai kuma babban abokin hamayyarsa, Pedro Pichardo na Portugal, yana nan a biye da shi, kuma zakaran gasar Olympics da na duniya yana cikin yanayi mai kyau, bayan da ya kafa tarihin kasa a lokacin da ya lashe gasar cikin gida ta Turai a watan Maris.

Haka nan kuma ‘yar kasar Zango, Marthe Koala, wadda ta yi tsallen tsayin mita 6.94, ita ce ta goma a duniya a kakar wasa ta bana a cikin tsalle mai tsayi – alamar da ke nuna cewa ba lallai ta iya lashe zinari ba, amma watakila ya tabbatar da cewa kasar ta mai da hankali kan wasannin tsalle-tsalle yayin ta ke hangen samun nasara a wasannin motsa jiki.

Najeriya ta samu lambar zinari ta farko a gasar cin kofin duniya da aka yi a Oregon ta hannun Tobi Amusan, inda ‘yar wasan tseren mita 100 ta kafa tarihi a wasan daf da na kusa da karshe a kan hanyarta ta zuwa daukaka.

Nigerian long jumper Ese Brume

Asalin hoton, Getty images

Sai dai 'yar shekaru 26, wadda itama ta lashe gasar Commonwealth, da wuya ta kasance a Budapest bayan da hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta tuhume ta da laifin rashin gwajin maganin kara kuzari guda uku - zargin da ta musanta. Amusan na fatan samun izini na, amma da alama wannan tsere ne da lokacin da ba za ta iya yin nasara ba.

A madadinta, ‘yar kasar Ese Brume na iya yunkurowa, inda ‘yar wasan tsalle ta kare da azurfa a Oregon ta hada da tagulla da ta samu daga wasannin Olympics na Tokyo da Gasar Doha ta Duniya a 2019.